WASANNI
2 MINTI KARATU
Manchester City ta sake daukar Kofin Gasar Firimiya
Arsenal ta kwashe galibin kakar wasa ta bana tana bayan City da maki hudu inda take da sauran wasa daya bayan Forest ta doke ta da ci 1-0.
Manchester City ta sake daukar Kofin Gasar Firimiya
Man City tana da damar daukar karin Kofuna biyu: Kofin FA da na Gasar Zakarun Turai. Hoto/Getty Images / Others
20 Mayu 2023

Manchester City ta yi nasarar lashe Kofin Gasar Firimiya karo na uku a jere bayan Arsenal ta sha kashi a hannun Nottingham Forest a wasan da suka yi a yau Asabar.

Arsenal ta kwashe galibin kakar wasa ta bana tana bayan City da maki hudu inda take da sauran wasa daya bayan Forest ta doke ta da ci 1-0.

Yaran Pep Guardiola sun lashe Kofin sau biyar a cikin kakar wasa shida da suka gabata.

Manchester City ta dauki fansa a kan Real Madrid

Baya ga wannan, City na da damar daukar karin Kofuna biyu a kakar bana: Kofin FA da kuma na Gasar Zakarun Turai a watan gobe.

Manchester United kadai ta taba yin irin wannan bajintar a kakar wasa ta 1998-99, kuma za ta fafata da ita a Wembley ranar 3 ga watan Yuni don neman daukar kofin FA, sannan ta gwabza da Inter Milan mako daya bayan haka a Istanbul domin neman lashe gasar Zakarun Turai karon farko.

Gobe Lahadi 'yan wasan City za su yi bikin daga Kofin nasu bayan sun fafata da Chelsea.

MAJIYA:TRT Afrika
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us