WASANNI
2 MINTI KARATU
Cristiano Ronaldo ya yi sujjada bayan ya ci kwallo
Dandazon ‘yan kallo sun rika sowa da murna a yayin da shahararren dan kwallon kafar ya rusuna ya yi sujjada bayan ya ci kwallo a wasan da Al Nassr ta doke Al Shabab da ci 3-2.
Cristiano Ronaldo ya yi sujjada bayan ya ci kwallo
Yanzu Al Nassr tana da maki 63, inda take bayan Al Ittihad FC, wadda ke ta daya, da maki uku a saman teburin babbar gasar kwallon kafa ta Saudiyya.  Hoto: Reuters / Others
24 Mayu 2023

Cristiano Ronaldo ya yi sujjada bayan ya zura kwallo a ragar kungiyar kwallon kafa ta Al Shabab a Gasar cin Kofin Kwararru da ake yi a Saudiyya.

Ana yin sujjada ne domin nuna godiya da girmamawa ga Allah.

A fafatawarsa ta mako na 28 ranar Talata, Ronaldo ya ci wa Al Nassr kwallo ta uku a minti na 59 sannan ya yi sujjada a filin wasa na KSU da ke Riyadh, kuma nan take ‘yan kallo suka barke da sowa da murna bisa abin da ya yi.

Ronaldo ya kure tarihin da ya kafa na wadda ya fi taka leda

‘Yan wasan Al Nassr Anderson Talisca da Abdurrahman Garib kowane ya zura kwallo daya, yayin da Cristian Guanca ya ci wa Al Shabab abin da ya sa aka tashi da ci 3-2.

Yanzu Al Nassr tana da maki 63, inda take bayan Al Ittihad FC, wadda ke ta daya, da maki uku a saman teburin babbar gasar kwallon kafa ta Saudiyya.

MAJIYA:TRT World
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us