DUNIYA
2 MINTI KARATU
Shugaba Biden ya yi tuntube ya fadi a bainar jama'a
Biden, mai shekara 80, wanda ya gabatar da jawabi a lokacin bude bikin, ya sha hannu da wani soja sannan ya koma kujerarsa bayan ya fadi.
Shugaba Biden ya yi tuntube ya fadi a bainar jama'a
Rahoton da likitocin Shugaba Biden suka fitar a wannan shekara ya ce yana da koshin lafiya kuma yana motsa jiki a-kai-a-kai / Hoto: AFP / Others
2 Yuni 2023

Shugaba Joe Biden ya runtuma a kasa bayan ya yi tuntube a yayin bikin yaye daliban sojojin sama na Makarantar Air Force Academy da ke birnin Colorado, amma da alama bai ji rauni ba — kuma ma daga bisani ya yi raha kan lamarin.

Biden, mai shekara 80, wanda ya gabatar da jawabi a lokacin bude bikin, kuma ya sha hannu da sojojin da aka yaye.

Wani sojin sama ne ya taimaka masa wajen tashi bayan ya fadi kuma da alama bai ji rauni ba.

A yayin da yake tashi, Biden ya nuna abin da ya taka ya sa shi yin tuntube. Ya yi kama da wani karamin kunshin jakar leda a kan dandamali.

"Na taka wani karamin kunshi," a cewar shugaban yayin da yake hira da manema labarai cike da murmushi bayan ya koma fadar White House ranar Alhamis sannan ya yi tattaki zuwa gidansa.

Daraktan Sadarwa na White House Ben LaBolt ya wallafa sakon Twitter inda ya ce shugaban kasar "yana cikin koshin lafiya. Ya taka wata karamar jakar leda a dandamali yayin da yake shan hannu da mutane."

MAJIYA:TRT World
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us