WASANNI
2 MINTI KARATU
Manchester City ta lashe FA Cup
Ilkay Gundogan ne ya zura dukkan kwallayen biyu, a yayin da Manchester City ta lashe kofi na biyu a kakar wasan bana ya zuwa yanzu.
Manchester City ta lashe FA Cup
Ilkay Gundogan ne ya zura dukkan kwallayen biyu. Hoto/Getty / Others
3 Yuni 2023

Manchester City tana kan hanyar daukar kofuna uku a kakar wasa ta bana bayan da kyaftin din kungiyar Ilkay Gundogan ya zura kwallo biyu da suka ba ta nasarar lashe Kofin FA.

City ta doke United da ci 2-1 a fafatawar da suka yi ranar Asabar a filin wasa na Wembley.

Gundogan ya zura daya daga cikin kwallayen ne a cikin dakika 12 da soma wasa, abin da ya sa ta zama kwallo mafi sauri da aka ci a tarihin gasar FA.

Manchester United ta farke kwallon da aka zura mata ta hannun Bruno Fernandes a minti na 33.

Amma Ilkay ya sake zura kwallo a ragar United a minti na 51.

Tuni dai City ta dauki Kofin Gasar Firimiya, don haka yanzu abin da ya rage mata shi ne Kofin Zakarun Turai inda za ta fafata da Inter Milan a makon gobe a Istanbul don nemansa.

Idan ta lashe shi za ta bi sahun United, wadda a 1999 ta lashe kofunan uku a kakar wasa daya.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us