AFIRKA
2 MINTI KARATU
Italiya ta taimaka wa Nijar da CFA biliyan biyu don bunkasa noman tumatur
Za a samar wa manoman wata hanyar ban ruwa ta hanyar amfani da hasken rana, musamman a jihohin Tawa da Maradi.
Italiya ta taimaka wa Nijar da CFA biliyan biyu don bunkasa noman tumatur
Italiya ta yi hakan ne da nufin shawo kan matsalar tsadar tumatur ko kuma yankewar sa a kasuwanni /Hoto: TRT Afrika / Others
22 Yuni 2023

Kasar Italiya ta taimaka wa Jamhuriyar Nijar da kudi sama da biliyan biyu na CFA domin bunkasa noman tumatur a kasar.

Italiya ta yi hakan ne da nufin shawo kan matsalar tsadar tumatur ko kuma yankewar sa a kasuwanni da ake gani a wasu lokutan a cikin shekara a Nijar din.

Wannan shirin bunkasa noman na tumatur a karkashin wannan tallafi na Italiya, ya kuma tanadi kaddamar da aikin noman tumatur a lambuna da fadinsa ya kai eka 100.

Za a samar wa manoman wata hanyar ban ruwa ta hanyar amfani da hasken rana, musamman a jihohin Tawa da Maradi.

Jamhuriyar Nijar na samar da tumaturin ne ta hanyar noman rani kawai, hakan ya sa ake yawan fuskatar karancinsa a lokuta da dama ciki kuwa har da lokacin damina.

Nijar tana da Kogin Isa da ya ratsa kasar har na tsawon kilomita 550 wanda yake taimaka wa wajen noman rani.

MAJIYA:TRT Afrika
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us