AFIRKA
2 MINTI KARATU
Kamfanin NNPC ya ciyo bashin dala biliyan uku daga bankin AFREXIM
NNPC ya ciyo bashin gaggawa ne don biyan kudin danyen mai, kuma ya bayyana cewa bashin zai rage matsin da Naira ke fuskanta a kasuwar canjin kudi.
Kamfanin NNPC ya ciyo bashin dala biliyan uku daga bankin AFREXIM
An sanya hannu kan yarjejeniyar bashin ne a hedikwatar bankin da ke birnin Alkahira na kasar Masar a ranar Laraba./Hoto: NNPCL / Others
16 Agusta 2023

Kamfanin mai na Nijeriya, NNPC Limited ya sanar da sanya hannu kan yarjejeniyar ciyo bashin gaggawa daga bankin raya kasuwancin shiga da fitar da kayayyaki na Afirka, wato AFREXIM Bank.

Bashin, wanda ya kai dala biliyan uku, za a yi amfani da shi wajen biyan bashin da ake bin kamfanin na NNPC na danyen mai.

An sanya hannu kan yarjejeniyar bashin ne a hedikwatar bankin da ke birnin Alkahira na kasar Masar a ranar Laraba, kamar yadda NNPCL ya wallafa a shafinsa na X wanda a baya ake kira Twitter.

Bankin na AFREXIM zai samar da kudin nan take don bai wa NNPCL dama ya tallafa wa tsarin gwamnatin tarayya kan hada-hadar kudi da haraji, da daidaita darajar Naira.

MAJIYA:TRT Afrika
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us