AFIRKA
2 MINTI KARATU
Burkina Faso ta umarci wakilin Faransa ya fita daga kasar
Hukumomin Burkina Faso sun zargi Pasquier da gudanar da “ayyukan da ke yin kafar-ungulu” ga kasar.
Burkina Faso ta umarci wakilin Faransa ya fita daga kasar
Kazalika Burkina Faso ta sanar da Faransa cewa za ta yi gaggawar rufe ofishin sojojinta da ke Paris ./Hoto:Reuters / Others
16 Satumba 2023

Gwamnatin mulkin sojin Burkina Faso ta umarci jami'in sojin Faransa da ke aiki a ofishin jakadancinta na kasar Emmanuel Pasquier ya tattara kayansa ya fita daga kasar nan da mako biyu.

Kafafen watsa labaran kasar ne suka rawaito hakan ranar Juma'a.

"An kori jami'in tsaron tare da sauran jami'an tsaro da ke ofishin sojin Faransa da ke babban birnin kasar Ouagadougou,” kamar yadda gidan rediyon Omega ya ambato wata sanarwa da hukumomin kasar suka aike wa ofishin jakadancin Faransa da ke kasar.

An zargi Pasquier da gudanar da “ayyukan da ke yin kafar-ungulu” ga kasar.

Kazalika wata sanarwa da Ma'aikatar Harkokin Wajen Burkina Faso ta fitar ta shaida wa Faransa cewa Burkina za ta yi gaggawar rufe ofishin sojojinta da ke Paris, a cewar rahoton.

Dangantaka ta yi tsami tsakanin Faransa da Burkina Faso bayan juyin mulkin watan Satumba na 2022 wanda ya dora Kaftin Ibrahim Traore a kan mulki.

A watan Janairu Burkina Faso ta daina huldar soji da Faransa, sannan ta bai wa tsohuwar uwar gajiyarta wata daya ta janye dakarunta daga kasar inda ta dade tana yaki da kungiyoyin ta'addanci irin su al-Qaeda da Daesh/ISIS.

MAJIYA:AA
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us