Cikin hotuna: Gwagwarmayar rayuwa a cikin yaki da sanyi a Gaza
Cikin hotuna: Gwagwarmayar rayuwa a cikin yaki da sanyi a Gaza
Falasdinawa a Gaza na ci gaba da rayuwa cikin mawuyacin hali a yayin da Isra'ila ke ci gaba da kai musu hare-hare.
19 Disamba 2023

Daga Charles Mgbolu

Labarin rayuwa a Gaza ba shi da dadin ji inda mutane da dama ke rayuwa a sansanoni budaddu, ga rashin isasshen abinci da ruwan sha.

Isra'ila ta kashe kusan Falasdinawa 20,000 tun 7 ga Oktoba, kuma mafi yawan wadanda ta kashe mata da yara kanana ne.

Idan dare ya yi, yanayi na yin sanyi sosai, da asuba mutane na farkawa cikin dimauta da yadda za su rayu zuwa yammaci.

Suna amfani da murhun duwatsu wajen dafa abinci da gasa burodi. SUna kuma amfani da wannan dama wajen jin dumi.

Busassun ciyawa da kirare ne suke amfani da su a matsayin mai na girki, kuma girkin ba ya sauri, amma kuma babu wani zabi da ya wuce wannan din, saboda an riga an kaste bayar da lantarki da man fetur a yankin.

Samun garin fulawar da za a yi burodi da shi ma na wahala sosai a kowacce rana.

'Yan jaridu da ke yankin sun ce motocin dakon kayan agaji ba sa iya zuwa yankin d ka yi wa ruwan bama-bamai inda mafi yawan jama'a suka koma bara da rokon burodi.

Har yanzu mutane na tattaunawa, a koyaushe sannan yara kanana na yin murmushin karfin hali.

An mayar da yunwa wani babban makami a yakin, Falasdina na bukatar juriya sosai don iya ci gaba da rayuwa.

MAJIYA:TRT Afrika
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us