WASANNI
2 MINTI KARATU
Super Eagles za ta fafata da Angola bayan ta cire Kamaru daga AFCON
Tawagar kwallon kafar Super Eagles ta Nijeriya za ta fafata da Angola a wasan dab da na kusa da karshe bayan ta doke Kamaru da ci 2-0 a wasan sili-daya-kwale a gasar cin kofin Afirka ranar Asabar.
Super Eagles za ta fafata da Angola bayan ta cire Kamaru daga AFCON
Ademola Lookman ne ya zura duka kwallayen biyu kafin da kuma bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.   Hoto:Super Eagles/X / Others
27 Janairu 2024

Tawagar kwallon kafar Super Eagles ta Nijeriya za ta fafata da Angola a wasan dab da na kusa da karshe bayan ta doke Kamaru da ci 2-0 a wasan sili-daya-kwale a gasar cin kofin Afirka ranar Asabar.

Ademola Lookman ne ya zura duka kwallayen biyu kafin da kuma bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Wasan ya fi zafi sosai inda Semi Ajayi ya ci kwallo amma alkalin wasa ya soke ta.

Nijeriya za ta gwabza da Angola, wadda ta doke Namibia da ci 3-0 a Bouake, ranar 2 ga watan Fabrairu.

Nijeriya ta tsallake zuwa matakin sili-daya-kwale ne bayan da ta zo matsayi na biyu a rukunin farko da maki bakwai.

MAJIYA:TRT Afrika
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us