WASANNI
2 MINTI KARATU
Super Eagles ta doke  Black Stars ta Ghana a wasan sada zumunta
Wannan ne karon farko da Nijeriya ta doke Ghana a wasan sada zumunta tun shekarar 2006.
Super Eagles ta doke  Black Stars ta Ghana a wasan sada zumunta
Ƴan wasan Nijeriya sun taka rawar gani sosai a fafatawar wadda aka yi a filin wasa na Stade de Marrakech ko da yake babu ƴan kallo da yawa./Hoto: Super Eagles / Others
23 Maris 2024

Tawagar ƙwallon ƙafar Nijeriya wato Super Eagles ta doke babbar abokiyar hamayyarta a Afirka Ghana da ci 2-1 a wasan sada zumunta da suka buga a birnin Marrakech ranar Juma'a.

Ɗan wasan Nijeriya Cyriel Dessers ne ya soma zura ƙwallo a zagayen farko yayin da Ademola Lookman ya ci ƙwallo ta biyu bayan an dawo daga hutun rabin lokaci.

Ɗan wasan Black Stars Jordan Ayew ya ci wa Ghana tata ƙwallon.

An bai wa ɗan wasan da ke tsaron baya na Ghana Jerome Opoku jan-kati lamarin da ya sa tawagar Black Stars ta gama wasan da ƴan wasa 10.

Ƴan wasan Nijeriya sun taka rawar gani sosai a fafatawar wadda aka yi a filin wasa na Stade de Marrakech ko da yake babu ƴan kallo da yawa.

Wannan ne karo na farko da Nijeriya ta doke Ghana a wasan sada zumunta tun shekarar 2006.

MAJIYA:TRT Afrika
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us