WASANNI
3 MINTI KARATU
Wasan zumunta: Mali ta karya lagon Nijeriya bayan shekara 49
Masu sharhi sun ce wannan ne karo na farko da tawagar ƙwallon ƙafa ta Mali ta yi galaba kan ta Nijeriya, bayan kusan shekaru 49.
Wasan zumunta: Mali ta karya lagon Nijeriya bayan shekara 49
Tawagar Super Eagles da ta kara da Mali ta sauya 'yan wasa. / Hoto: NFF TV / Others
27 Maris 2024

Bayan da tawagar ƙwallon ƙafa ta Mali ta samu nasara kan tawagar Nijeriya da ci 2-0 a daren Talata, rahotanni sun nuna cewa nasarar ita ce karon farko tun bayan kusan shekaru 50 Mali tana shan kashi a hannun Nijeriya.

El Bilal Toure ne ya ciyo wa Mali ƙwallo ta farko kafin hutun rabin lokaci, sai a zango na biyu na wasan, Kamory Doumbia ya zura ƙwallo ta biyu.

An buga wasan na sada zumunta a filin wasa da ke birnin Marrkesh na ƙasar Maroko.

Bayan wasa, kocin Super Eagles, Finidi George ya faɗa wa manema labarai cewa, "Kurakurai ne suka janyo mana rashin nasara amma ba za a ce wasan bai yi kyau ba. Mun samar da damarmaki, duk da dai ba mu ci ƙwallo ba."

'Ba iyawa aka fi mu ba'

Finidi ya ƙara da cewa, "Na yi murna da yadda yaranmu suka yi wasa. Ba wasa aka fi mu iya ba, amma dai na so a ce ba haka sakamakon wasan ya ƙare ba."

Mali, wadda ta zo matakin kusa da na ƙarshe a gasar kofin Afirka ta fi ƙoƙari a zangon farko na wasan inda Toure ya ci ƙwallo bayanwani kuskuren da ɗan wasan baya na Nijeriya ya yi.

Bayan hutun rabin lokaci ne Nijeriya ta kankane wasan, amma ba su samu nasarar cin ƙwallo ba har lokacin da ɗan wasan Mali, Doumbia ya ciyo wa Mali ƙwallo ta biyu, inda aka tashi suna da ci biyu da nema.

A gasar cin kofin Afirka ta 2023 da aka yi a Ivory Coast, Nijeriya ce ta zo ta biyu bayan da a wasan ƙarshe, ƙasa mai masaukin baƙi ta doke ta, ta kuma lashe kofin.

MAJIYA:TRT Afrika
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us