DUNIYA
1 MINTI KARATU
Ba a ga watan Ƙaramar Sallah ba a Saudiyya
Hukumomi a Saudiyya sun ce ba a ga watan Shawwal ba a ƙasar don haka sai ranar Laraba za a yi Ƙaramar Sallah.
Ba a ga watan Ƙaramar Sallah ba a Saudiyya
Hakan na nufin ba za a yi Ƙaramar Sallah sai ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu. . / Hoto: Getty Images / Others
8 Afrilu 2024

Hukumomi a Saudiyya sun ce ba a ga watan Shawwal ba a ƙasar ranar Litinin, 29 ga watan Ramadan shekarar 1445, daidai da takwas ga watan Afrilu, 2024.

Sun bayyana haka ne a sanarwar da aka wallafa a shafin Haramain wanda ke kula da masallatai masu tsarki.

Hakan na nufin ba za a yi Ƙaramar Sallah sai ranar Laraba, 10 ga watan Afrilu.

MAJIYA:TRT Afrika
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us