AFIRKA
3 MINTI KARATU
Ɓangarorin da ke yaƙi da juna a Sudan sun haɗu a Geneva don tattaunawar tsagaita wuta da MDD ta shirya
Tun watan Afrilun 2023 ne ake ta gwabza yaƙi tsakanin Sojojin Sudan da Dakarun sa kai na RSF a ƙasar, lamarin da ya raba kusan mutane miliyan 10 da mastugunansu tare da jefa su cikin barazanar haɗarin yunwa.
Ɓangarorin da ke yaƙi da juna a Sudan sun haɗu a Geneva don tattaunawar tsagaita wuta da MDD ta shirya
Sojojin Sudan da dakarun RSF za su yi zaman "tattaunawa" ta hanyar masu shiga tsakani a maimakon ganawa ido da ido, in ji wakiliyar MDD ta musamman./ Hoto: AFP  / Others
12 Yuli 2024

Ɓangarorin da ke rikici da juna a Sudan sun isa birnin Geneva na ƙasar Switzerland domin tattaunawa kan ''yiwuwar tsagaita wuta a kasar'' wanda Majalisar Ɗinkin Duniya ta shirya da nufin sauƙaƙa ayyukan jin kai da kare fararen hula, in ji mai magana da yawun MDD.

Yaƙin Sudan, wanda ya ɓarke a watan Afrilun 2023 ya tilasta wa mutane kusan miliyan 10 barin matsugunansu, lamarin da ya haddasa barazanar yunwa da rikice-rikice na ƙabilanci waɗanda aka ɗora alhakinsa kan ƙungiyar Rapid Support Forces (RSF).

Yarjejeniyar da aka ƙulla a birnin Jeddah na ƙasar Saudiyya tsakanin Sojojin Sudan da dakarun sa kai na RSF wacce Amurka da Saudiyya suka jagoranta a ƙarshen shekarar bara ta wargaje.

''Zaman tattaunawar zai mayar da hankali ne kan lalubo hanyoyin ci gaba da ayyukan jin kai da kuma kare fararen hula ta hanyar tsagaita wuta a ƙasar, kamar yadda Kwamitin Sulhu na Majalisar Dinkin Duniya ya buƙata,'' a cewar mai magana da yawun MDD sa'ilin da take amsa tambayoyin kamfanin dillancin labarai na Reuters.

A cewarta, wakilin Majalisar Dinkin Duniya a Sudan Ramtane Lamamra daga Aljeriya ne ya shirya zaman tattaunawar da aka soma a ranar Alhamis.

Sojojin Sudan da dakarun RSF za su yi zaman "tattaunawa" ta hanyar masu shiga tsakani a maimakon ganawa ido da ido, in ji ta.

Jakadiyar Amurka a MDD Linda Thomas-Greenfield ta shaida wa gidan talabijin na CBS cewa, an gayyaci wakilin Amurka na musamman a Sudan Tom Perriello don shi ma yana daga masu zaman tattaunawar a Geneva wanda ya mayar da hankali kan ''yadda za a magance barazanar da ayyukan jin ƙai ke fuskanta da taimaka wa mabuƙata da nemo mafita kan matsalar siyasa domin haɗa ɓangarorin biyun da ke yaƙi da juna wuri guda.''

MAJIYA:TRT World
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us