TURKIYYA
10 MINTI KARATU
Turkiyya: Muhimman abubuwan tuni a yunƙurin juyin mulkin ranar 15 ga Yuli
Daga rufe hanyar gadoji da filin jirgin sama zuwa ga kai hare-hare gidan watsa labarai na gwamnati da majalisar dokoki da kuma fadar shugaban ƙasa, ga abubuwan da suka faru a ɗaya daga cikin dare mafi tsawo a Turkiyya.
Turkiyya: Muhimman abubuwan tuni a yunƙurin juyin mulkin ranar 15 ga Yuli
Yunkurin juyin mulkin da bai yi nasara ba a shekarar 2016 wata muhimmiyar nasara ce ga al'ummar ƙasar Turkiyya domin wannan shi ne karo na farko a tarihin kasar da yunkurin juyin mulki na soji bai yiwu ba, sannan kuma aka samu nasarar kafa dimokradiyya. / Hoto:AA / Others
15 Yuli 2024

Shekaru takwas ke nan tun bayan da manyan motocin sojoji suka mamaye gadojin Istanbul sannan jiragen yaki suka yi shawagi tare da luguden wuta kan fararen-hula a Turkiyya.

A daren ranar 15 ga Yuli, 2016, Turkiyya ta shiga wani mummunan yanayi na yunƙurin juyin mulki.

An bayyana wadanda suka yi yunƙurin juyin mulkin da ƙungiyar ta'addanci ta FETO (Fetullah) wadda ta kaddamar da shirinta kafin lokacin da aka tsara saboda wasu bayanan sirrinsu da suka fito fili.

Jerin manyan abubuwan da suka faru sun fi mai da hankali a Istanbul da Ankara inda aka kai hare-hare tare da rufe hanyoyin gadoji da jirage masu saukar ungulu da suka yi ta sauka kasa-kasa lamarin da ya haifar da hargitsi da tashin hankali .

A yayin da dare ya soma sauka a ranar, fitattun mutane ciki har da shugaban ƙasar Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, sun yi kira ga al'ummar kasar da su bijire wa yunƙurin juyin mulki, lamarin da ya sa fararen-hula suka fito don daukar mataki.

A ƙarshe dai an dakile yunƙurin, amma an samu asara mai yawa da kuma tashin hankali.

Lamarin dai ya yi sanadiyar mutuwar fararen-hula 253 tare da jikkata sama da mutum 2,700.

Ga lokutan jerin abubuwan da suka faru da kuma muhimman abubuwan za a iya tunawa da su:

12:22 RANA

Masu yunƙurin sun aika da tsare-tsaren shirinsu na yunkurin juyin mulkin zuwa sassa daban-daban da ke ƙarkashinsu.

4:00 RANA

Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya (MIT) ta sanarwa ofishin ma'aikatan gwamnatin Turkiyya game da yiwuwar yunƙurin juyin mulkin.

Ba a bayyana wa al'umma inda Erdogan yake ba a Marmaris har sai da yunƙurin juyin mulkin ya fito fili.

9:00 DARE

Sakamakon sirrinsu da ya fito fili, masu yunƙurin juyin mulkin sun fara aiwatar da yunƙurinsu da wuri kafin ainihin lokacin da aka tsara.

9:30 DARE

Erdogan ya samu ƙiran wayar tarho kan ayyukan soji da ba saba gani ba, lamarin da ya sa ya tuntubi wasu manyan jami'ai, ciki har da shugaban hukumar MIT na wancan lokacin Hakan Fidan da kuma shugaban rundunar sojin Turkiyya Janar Hului Akar.

Rufe hanyar gadojin Istanbul

10:00 DARE

Sojojin da suka yi yunkurin sun rufe gadar Bogazici na Istanbul da Fatih Sultan Mehmet.

Jirgin F-16 ya fara shawagi kasa-kasa a Ankara.

Erdogan ya isa wurin shugaban MIT Hakan Fidan a wannan lokacin don samun ƙarin bayani game da yanayin abubuwan da ke faruwa.

11:00 DARE

Binali Yildirim, firaministan lokacin, ya sanar da yunƙurin juyin mulkin a gidan talabijin ɗin NTV na Turkiyya.

Sojojin da suka yi yunƙurin juyin mulkin sun bude wuta kan fararen hula da ke adawa da juna a gundumomin Cengelkoy da Sarachane na Istanbul.

11:45 DARE

An dakatar da tashin jirage a filin jirgin sama na Ataturk.

An sanar da Erdogan game da jiragen soji da ke shawagi a kasa-kasa a birnin Ankara.

11:50 DARE

Jama'a sun fara cika a kan tituna suna zanga-zanga.

12:00 TSAKAR DARE

Majiyoyin tsaro sun bayyana cewa dakarun ƙungiyar FETO ne suka kitsa yunkurin juyin mulkin.

An kai hari hedikwatar Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya MIT.

12:09 TSAKAR DARE

Wani jirgin sama mai saukar ungulu ya bude wuta kan ofishin hukumar leken asiri ta kasa (MIT) a Ankara.

Erdogan ya yi koƙarin tuntubar wasu manyan jami'ai kamar Janar Hulusi Akar, wanda daga baya aka bayyana cewa masu yunkurin juyin mulkin sun yi garkuwa da shi.

12:13 TSAKAR DARE

An tilasta wa Tijen Karas ma'aikacin kafar yada labarai na TRT karanta sanarwar juyin mulkin.

12:37 TSAKAR DARE

Shugaban ƙasar Turkiyya Erdogan ya yi wa al'ummar kasar jawabi ta hanyar bidiyon kai tsaye ta gidan talabijin na CNN Turk, inda ya bukaci 'yan kasar da su fito kan tituna.

“Mu taru a dandalinmu da filayen jiragen sama - mu bar su su zo da tankunansu da motocin igwa, su yi abin da za su yi.

Har yanzu ban ga ƙarfin da ya wuce na al'umma ba,'' in ji Erdogan.

12:40 TSAKAR DARE

Masallatai sun yi ta addu'o'i, suna kira ga 'yan kasar da su yi adawa da juyin mulkin.

12:50 TSAKAR DARE

Kamfanin dillancin labarai na Anadolu ya bayar da rahoton cewa, an yi garkuwa da babban hafsan hafsoshin sojin kasar Hulusi Akar.

Hare-hare kan TURKSAT

12:57 TSAKAR DARE

Sojojin sun yi ƙoƙarin kwace ma'aikatar sadarwa ta TurkiyaTURKSAT don yanke hanyoyin sadarwa a cikin ƙasar.

1:00 TSAKAR DARE

Sojojin sun kai hari a otal ɗin da shugaba Erdogan ya sauka.

1:39 TSAKAR DARE

Shugaban majalisar ɗokokin ƙasar Ismail Kahraman da 'yan majalisa daga jam'iyyar AKP da CHP da kuma MHP sun hallara a zauren majalisar da ke Ankara.

1:50 TSAKAR DARE

Wasu daga cikin sojojin da ke da hannu a yunƙurin juyin mulkin sun fara mika wuya.

2:16 TSAKAR DARE

Sajan Omer Halisdemir ya kashe jagoran juyin mulkin Manjo Semih Terzi a hedikwatar runduna ta musamman.

2:20 TSAKAR DARE

Mayakan juyin mulkin sun kai harin sama kan hedikwatar rundunar Golbasi ta musamman, inda suka kashe jami’an ‘yan sanda hamsin.

2:30 TSAKAR DARE

Jama'a da 'yan sanda sun kori masu yunƙurin juyin mulki daga gidan talabijin na ƙasa TRT, inda aka ci gaba da yada shirye-shiryen.

Sannan ba a yi nasara wajen kwace MIT da fadar shugaban kasa ba.

Harin Bam a majalisar ɗokokin Turkiyya

2:42 TSAKAR DARE

An jefa bam na farko a Majalisar, lamarin da ya sanya 'yan majalisar neman mafaka.

3:20 TSAKAR DARE

Jirgin Erdogan ya sauƙa a filin jirgin saman Ataturk a cikin yanayi da ake ciki na tashin hankali, yana mai cewa: ''Abin da ke da muhimmanci ba wai kasancewa ta anan ba ne, amma kasancewarku a nan.''

6:00 SAFE

Sojojin yuƙurin juyin mulkin a gadar Bogazici sun mika wuya.

6:43 SAFE

A jefa bam na biyu a harabar fadar shugaban ƙasa da ke Bestepe.

7:00 SAFE

An jefa wani bam a kusa da rundunar Gendarmerie da ke kusa da harabar fadar shugaban kasa.

8:32 SAFE

Wani samame da aka yi a filin jiragen sama na 'Akinci Main Jet Base Command' da ke Ankara ya kai ga sakin Hulusi Akar. Bayan haka.

Sauran masu yunkurin juyin mulkin a fadin kasar sun fara mika wuya.

MAJIYA:TRT World
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us