AFIRKA
1 MINTI KARATU
Mali ta bai wa jakadan Sweden awa 72 ya bar ƙasarta
Umarnin na zuwa ne bayan da Sweden ta sanar da kawo ƙarshen tallafin da take bai wa Mali.
Mali ta bai wa jakadan Sweden awa 72 ya bar ƙasarta
Ma'aikatar Harkokin Wajen Sweden ba ta ce komai ba tukunna a kan batun. / Hoto: AFP
9 Agusta 2024

Ma'aikatar Harkokin Wajen Mali ta bai wa jakadan ƙasar Sweden umarnin barin ƙasarta cikin awa 72 a ranar Juma'a, kan abin da ta kira "wasu kalamai marasa daɗi" da wani ministan Sweden ya yi.

A ranar Laraba ne Ministan Sweden na cigaban hadin kan ƙasa da ƙasa da kasuwanci Johan Forssell, ya ce gwamnatin ƙasarsa ta yanke shawarar daina bai waMali tallafi.

Ma'aikatar Harkokin Wajen Sweden ba ta ce komai ba tukunna a kan batun.

Mali da maƙwabtanta Nijar da Burkina Faso sun ƙulla alaƙa ta ƙut-da-ƙut da Rasha don tura haushi ga ƙasar da ta yi musu mulkin mallaka Faransa, da Nijeriya da kuma Amurka.

MAJIYA:Reuters
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us