DUNIYA
3 MINTI KARATU
Isra'ila ta kashe ƙarin mutum 47 a sabbin hare-hare a Gaza
A rana ta 331 da Isra’ila ta kwashe tana yaƙi a Gaza, ta kashe Falasɗinawa aƙalla 40,738 – galibinsu mata da yara – tare da jikkata fiye da 94,154 inda hasashe ya bayyana sama da mutum 10,000 na ƙarƙashin ɓaraguzan gidajen da aka yi wa ruwan bam.
Isra'ila ta kashe ƙarin mutum 47 a sabbin hare-hare a Gaza
Isra'ila na ci gaba da kashe Falasɗinawa a Gaza a kullum waɗanda akasarinsu mata ne da yara. / Hoto: AA
1 Satumba 2024

1018 GMT — Aƙalla Falasɗinawa 47 Isra’ila ta sake kashewa a Gaza, kamar yadda hukumomi suka tabbatar.

Zuwa yanzu adadin mutanen da Isra’ilar ta kashe a Gaza sun kai 40,738 sannan 94,154 suka jikkata a hare-haren da Isra’ila ke ci gaba da kaiwa tun daga 7 ga watan Oktoba.

0731 GMT — An soma gudanar da rigakafin cutar polio a hukumance a Gaza a daidai lokacin da Isra'ila ke ci gaba da luguden wuta a Gaza.

An sanar da soma wannan aikin rigakafin ne bayan da aka samu ɓullar cutar ta polio a karon farko a Gaza bayan shekara 25.

Jarirai sabbin haihuwa har zuwa shekara goma da haihuwa an kai su wuraren gudanar da rigakafin domin ba su, inda a daidai lokacin jirage marasa matuƙa suka rinƙa wucewa ta sama, in ji Yasser Shaabane, wanda darakta ne na kiwon lafiya a asibitin al-Awda da ke tsakiyar Gaza.

"Akwai jirage marasa matuƙa da dama da ke yawo a tsakiyar Gaza kuma muna fata za a gudanar da wannan rigakafin ga yara lafiya," in ji Shaabane.

0656 GMT — Sojojin Isra'ila sun kai wasu jerin samame a Hebron, lamarin da ya yi sanadin tsare Falasdinawa 6 da suka hada da mata uku.

A cewar kamfanin dillancin labarai na WAFA, an gudanar da samamen ne na musamman a birnin Hebron da garuruwan Halhul da ke arewa da kuma Yatta a kudu.

Majiyar ta ruwaito cewa sojojin na Isra'ila sun kai samame a garin Yatta tare da tsare wasu mazauna garin biyu ciki har da Yamama Ibrahim Hirini, wata daliba 'yar shekara 18 a Jami’ar Palestine Polytechnic University.

MAJIYA:TRT Afrika da abokan hulda
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us