WASANNI
2 MINTI KARATU
An tabbatar da ranar fara Gasar CHAN 2025 ta ƙasashen Afirka
Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF) ta saka ranar 1 zuwa 28 ga Fabrairun 2025, a matsayin ranakun buga gasar gida ta ƙasashen Afirka da za a yi a Kenya, Tanzania, da Uganda.
An tabbatar da ranar fara Gasar CHAN 2025 ta ƙasashen Afirka
Gasar CHAN  ta 2025 za ta zama ta farko da za ta gudana a gabashin Afirka. / Hoto: AFP / Others
17 Satumba 2024

Shugaban Hukumar Ƙwallon Ƙafa ta Afirka (CAF), Patrice Motsepe ya sanar ranar Litinin cewa an saka ranar 1 zuwa 28 ga Fabrairun 2025 a matsayin ranakun buga gasar ƙasashen Afirka ta takwas da za a yi a Kenya, Tanzania, da Uganda.

Gasar ta CHAN da ake duk bayan shekara biyu, tana taƙaita ne ga 'yan wasan da ke taka leda a cikin nahiyar Afirka kawai, inda ake haramta wa manyan 'yan wasa da ke buga wasa a Turai.

Wannan ne karo na farko da gabashin Afirka za ta karɓi baƙuncin gasar ta ƙungiyoyin ƙwallo na ƙasashen Afirka. Kuma gasar za ta share fagen gasar AFCON ta 2027 da za a gudanar a ƙasashen na gabashin Afirka uku.

Shugaban CAF, Motsepe ya ziyarci filayen wasa uku na Kenyan, waɗanda aka zaɓa don gudanar da gasar, inda biyu cikinsu ake musa gyare-gyare.

'Na gamsu'

Motsepe ya faɗa bayan jagorantar taron kwamitin zartarwa na CAF cewa, "Na gamsu da aniyar da ƙasashen uku suka nuna, kuma dukkansu suna da damar inganta kayayyakin ƙwallon ƙafa don janyo hankulan dubban maziyarta da masu yawon buɗe ido".

Za a fara wasannin neman cancantar shiga gasar da za ta ƙunshi tawagogi 19 ranar 25 ga watan Oktoba, sannan a kammala a ƙarshen Disamba.

Senegal ce ta lashe gasar da aka yi ta ƙarshe a 2023, inda suka doke Algeria wadda ta karɓi baƙuncin gasar da ci 5-4 a bugun ɗurme na wasan ƙarshe.

Morocco da DR Congo su ma sun ci gasar ta CHAN sau biyu, tun sanda aka fara ta a 2009.

MAJIYA:TRT Afrika
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us