AFIRKA
2 MINTI KARATU
Rwanda ta tabbatar da ɓullar cutar Marburg a karon farko a ƙasar
Cutar Marburg na saka zazzaɓi mai ƙarfi tare da yaɗuwa a tsakanin mutane, kamar dai yadda cutar Ebola take, in ji WHO.
Rwanda ta tabbatar da ɓullar cutar Marburg a karon farko a ƙasar
Ana kamuwa da cutar Marburg daga jemagun bishiyoyin kayan marmari. / Photo: Reuters / Others
30 Satumba 2024

Rwanda ta sanar da samun ɓullar cutar Marburg a karon farko a ƙasar, inda mutane takwas suka mutu bayan kamuwa da ita, in ji Ma'aikatar Lafiya a ranar Lahadi.

Ya zuwa 29 ga Satumba, an samu mutane 26 ɗauke da cutar a ƙasar da ke Gabashin Afirka, in ji ma'aikatar a sanawar da ta fitar ta shafin X.

"Mutane za su iya ci gaba da harkokinsu na yau da kullum - ba a hana gudanar da wani aiki ba a matsayin matakan magance cutar Marburg. Kar mutane su firgita a yayin da muka gano dukkan yankunan da cutar ta bulla kuma ana daukar matakan da suka kamata," in ji Ministan Lafiya na rwanda Sabin Nsanzimana a shafin X.

Cutar Marburg na saka zazzabi mai karfi tare da yaduwa a tsakanin mutane, kamar dai yadda cutar Ebola ta ke, in ji Hukumar Kula da Lafiya ta Duniya (WHO).

Ana ɗaukar cutar Marburg daga jemagun bishiyun kayan marmari kuma tana yaduwa a tsakanin mutane bayan cudanya da mai dauke da ita, ko taba wani waje da mai cutar ya taba.

MAJIYA:TRT Afrika
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us