WASANNI
3 MINTI KARATU
Neymar ya musanta barazanar korarsa saboda yawan tafiya jinya
Neymar Jr ya musanta raɗe-raɗin cewa Al-Hilal ta Saudiyya za ta soke kwantiraginsa saboda yawan tafiya jinya da yake yi.
Neymar ya musanta barazanar korarsa saboda yawan tafiya jinya
Neymar first training for Al Hilal after injury / Photo: Reuters
12 Nuwamba 2024

Bayan dawowar Neymar Jr daga jinyar shekara guda, a yanzu ɗan wasan na Al-Hilal ta Saudiyya ya sake tafiya wata jinyar ta mako shida. Hakan ya haifar da raɗe-raɗin cewa ƙungiyarsa za ta sallame shi, tare da soke kwantiraginsa.

Neymar wanda ɗan asalin Brazil ne da ya yi shuhura tun yana buga wasa a ƙasarsa, shi ne ɗan wasan tawagar Brazil da ya fi ciyo wa ƙasarsa ƙwallo a tarihi, bayan cin ƙwallo 79 a wasanni 128.

Ɗan wasan mai shekaru 32 ya buga wa manyan ƙungiyoyin Turai wasa, wato Barcelona da PSG, kafin ya koma taka leda a Saudiyya a shekarar 2023.

Sakamakon yawan samun rauni da yake samu wanda yake hana shi buga wasanni, PSG ta sayar da shi ga Al Hilal kan Fam miliyan €90, inda kwantiragin za ta ƙare a bazara mai zuwa.

Raɗe-raɗin cewa Neymar zai bar Al-Hilal ya saka an fara hasashen cewa zai bi tsohon abokin wasansa Lionel Messi wajen komawa Inter Miami ta Amurka, ko kuma tsohon kulob ɗinsa Santos a Brazil.

'Ina farin ciki'

A wani taro na neman Saudiyya ta samu damar ɗaukar nauyin gasar ƙwallon ƙafa ta duniya ta FIFA a 2034, Neymar ya bayyana cewa har yanzu yana cikin farin ciki a ƙungiyarsa ta Al-Hilal.

Ya ce "Ina matuƙar farin cikin kasancewa a nan, kuma na tabbata abubuwa za su ƙara kyau. Kuma na tabbata wasu taurarin ƙwallo za taho nan."

Duk da cewa Neymar bai buga mata wasa ba kusan tsawon gabaɗaya kakar bara, Al-Hilal ta lashe gasar Saudi Pro League a kakar ba tare da an doke ta ba.

Neymar ba zai dawo wasa ba sai a Disamba, sakamakon raunin da ya samu a tantanin gaɓarsa.

MAJIYA:TRT Afrika
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us