AFIRKA
2 MINTI KARATU
Tarayyar Turai ta yi wa jakadanta da ke Nijar kiranye
Wannan na zuwa ne bayan Nijar ɗin ta caccaki jakadan Tarayyar Turan inda ta zarge shi da raba kimanin euro miliyan 1.3 ga ƙungiyoyi masu zaman kansu a ƙasar ba tare da sanar da hukumomi ba.
Tarayyar Turai ta yi wa jakadanta da ke Nijar kiranye
Gwamnatin ta Nijar ɗin ta buƙaci a yi mata bayani dangane da yadda aka kasafta kuɗin. / Hoto: AA / Others
23 Nuwamba 2024

Ƙungiyar Tarayyar Turai ta yi wa jakadanta na Nijar kiranye sakamakon sojojin ƙasar sun caccaki ƙungiyar kan yadda take kai agaji ga ƙasar da ke Yammacin Afirka.

“Ƙungiyar EU ta yanke shawawar yi wa jakadanta da ke Yamai kiranye domin tattaunawa da shi a Brussels,” kamar yadda wani mai magana da yawun Tarayyar Turan ya yi bayani.

A ranar Juma’a ne Nijar ɗin ta zargi jakadan Tarayyar Turai da raba kimanin euro miliyan 1.3 ga ƙungiyoyi masu zaman kansu a ƙasar ba tare da sanar da hukumomin ƙasar ba.

Gwamnatin ta Nijar ta buƙaci a yi mata bayani dangane da yadda aka kasafta kuɗin.

Tun bayan ƙwace mulki a Yulin 2023, shugabannin soji da ke mulki a Nijar sun juya wa ƙasashen Yamma baya.

Haka kuma makwabtansu waɗanda suka haɗa da Burkina Faso da Mali su ma sun juya wa ƙasashen Yamman baya waɗanda suka haɗa da Faransa da Amurka.

MAJIYA:AFP
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us