DUNIYA
1 MINTI KARATU
Majalisar Tsaro ta Isra'ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza: Ofishin Firaminista
Ofishin firaminista ya ce idan aka cim ma yarjejeniyar, to tsagaita wutar za ta fara aiki a ranar Lahadi da zarar an saki kashin farko na fursunonin.
Majalisar Tsaro ta Isra'ila ta amince da yarjejeniyar tsagaita wuta ta Gaza: Ofishin Firaminista
A yanzu yarjejeniyar za ta je gaban majalisar a cike. / Hoto: AFP
17 Janairu 2025

Majalisar Tsaron Isra'ila ta amince da tsagaita wutar da zai dakatar da yaƙin da take yi da Hamas a Gaza tare da sakin fursunonin da dukkan ɓangarorin biyu ke tsare da su.

A yanzu yarjejeniyar za ta je gaban majalisar a cike.

Ofishin firaminista ya ce idan aka cim ma yarjejeniyar, to tsagaita wutar za ta fara aiki a ranar Lahadi da zarar an saki kashin farko na fursunonin.

MAJIYA:TRT World
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us