TURKIYYA
2 MINTI KARATU
Turkiyya ta taimaka wurin sakin 'yan ƙasar Thailand da aka yi garkuwa da su a Gaza
Majiyoyin diflomasiyya sun ce hukumar leken asiri ta Turkiyya tare da hadin gwiwar jami'an Thailand ne suka shirya kubutar da mutanen a yayin da suka ci gaba da tattauna wa da Hamas don sakin su.
Turkiyya ta taimaka wurin sakin 'yan ƙasar Thailand da aka yi garkuwa da su a Gaza
An ga ana mika 'yan kasar Thailand din da aka yi garkuwa da su ga hannun ma'aikatar Kungiyar Bayar da Agaji ta Red Cross (ICRC) by Hamas. / Photo: AA / Others
30 Janairu 2025

Hukumar Leken Asiri ta Turkiyya (MIT) ta yi nasarar ganin an saki wasu ‘yan kasar Thailand su biyar da aka tsare a Gaza, bayan yunkuri mai karfi na diflomasiyya da tattaunawa.

An saki mutanen a ranar Alhamis a wani bangare na ayyukan shiga tsakani da Turkiyya ke yi a yankin, in ji Ma’aikatar Harkokin Wajen Turkiyya.

Yunkurin diflomasiyyar Turkiyya

Bisa umarnin Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan, MIT ta yi aiki da jami’an Thailand tun a farkon yunkurin, inda suka ci gaba da tattaunawa da kungiyar tirjiya ta Falasdin, Hamas don sakin su, in ji ma’aikatar.

Diflomasiyyar Turkiyya a ayyukan leken asiri ta taka rawa sosai wajen tabbatar da mutanen sun dawo lafiya.

Shiga tsakani mai fadi

Sakin fursunonin yakin na zuwa ne a lokacin da ake aiki da tsagaita wuta tsakanin Hamas da Isra’ila da aka fara a ranar 13 ga Janairu 2025, wadda Turkiyya ta shiga tsakani don tabbatarwa.

Tare da kokarinta na shiga tsakani, MIT ta kuma yi aikin kwashe fararen hular da aka jikkata, ‘yan aksar Turkiyya da ‘yan wasu kasashen daga Gaza.

Turkiyya ta sake jaddada aniyarta na samar da zaman lafiya a yankinta, kokarin bayar da tallafin jin kai, da kare fararen hula, tare da kuma ci gaba da yin tattaunawar diflomasiyya don taimaka wa wadanda rikicin ya shafa.

MAJIYA:TRT World
Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us