Isra’ila na kashe jariran Falasdinawa a Gaza ‘don nishaɗi’ in ji tsohon janar din sojin ƙasar
GABAS TA TSAKIYA
4 minti karatu
Isra’ila na kashe jariran Falasdinawa a Gaza ‘don nishaɗi’ in ji tsohon janar din sojin ƙasarYair Golan ya bayyana cewa kasa mai hankali ba ta kai wa fararen hula hari, ba ta kashe jarirai don nishadi, ko kokarin korar jama’a ‘yan asalin yanki.
Tun watan Oktoban 2023 zuwa yau Isra'ila ta kashe yaran Falasdinawa 18,000, in ji Ma'aikatar Lafiya ta Falasdin. / AA
21 Mayu 2025

Dan siyasar adawa na Isra’ila kuma tsohon janar din sojin kasar, Yair Golan ya zargi Tel Aviv da kashe jaririan Falasdinawa don jin dadi kawai, kuma suna neman korar miliyoyin Falasdinawa da Gaza da aka yi wa kawanya.

“Kasa mai hankali…. ba za ta dinga kashe jarirai don nishadi ba,” in ji Golan a wata tattaunawa a rediyo a ranar Talata, wanda ya sanya gwamnatin Isra’ila da ‘yan adawa sukar sa.

“Isra’ila na kan hanyar zama saniyar ware - kamar tsihuwar Afirka ta Kudu - matukar dai ba ta dawo ta zama kas amai hankali ba,” in ji Golan, shugaban jam’iyyar Democrats ta Isra’ila.

“Kasa mai hankali ba ta kai wa fararen hula hari, ba ta kashe jarirai don nishadi, ko kokarin korar jama’a ‘yan asalin yankinsu,” ya fada a wata tattaunawa ta rediyo.

Netanyahu ya zargi Golan, tsohon manjo janar a sojin kasar, da “ingiza mutane” su yi wa dakarun Isra’ila bore da ma tsanar kasar.

Masu sukar gwamnati ma sun soki Golan, inda shugaban ‘yan adawa Yair Lapid ta shafinsa na X ya ce: “Mayakanmu jarumai ne kuma suna kare rayukanmu. Batun wai suna kashe jarirai don nishadi ba gaskiya ba ne kuma kyauta ce ga makiyanmu.”

Shugaban sojoji Eyal Zamir a wata sanarwa ya soki kalaman Golan da suke janyo tantama kan ayyuka da halayyar sojojin.

Da yake mayar da martani ga sukar, Golan ta shafinsa na X ya fadi cewa yana kokarin daga murya ne kan hanyar da ya ga Isra’ila na bi.

A wajen wani taron mnema labarai, Golan ya ce sukar da yake yi “ba ta nufar sojojin”.

“Sukar da nake yi na da manufar hankaltar da gwamnati, ba sai sukar sojoji ba, wanda gidana ne kuma suna cikin zuciyata,” ya fada wa ‘yan-jaridu.

“Gwamnatin da ta ce za ta bar fursunonin yaki da jefa yara cikin kangin yunwa, gwamnati ce da ke magana irin ta mai magana da yawun Hamas,” ya kara fada.

Golan, sanannen mai adawa da gwamnatin Netanyahu da manufofinta, tun bayan wani jawabi da ya yi a 2016 da ya ja layi tsakanin al’ummar Isra’ila da yadda nuna kyama ke daduwa a Turai a 1930 ya zama wanda ake ta ka ce na ce a kansa.

A watan Nuwamban 2024, ya zargi netanyahu da fifita bukatar kansa ta siyasa sama da bukatar kasar, bayan ya kori ministan tsaro Yoav Gallant.

Golan ya sake jaddada wa a ranar Talata yana cewa “A lokacin da ministocin gwamnatin nan ke murnar mutuwa da rasa abinci ga yara kanana, dole ne mu fadi haka. Ni ina magana ne kan gwamnatin Isra’ila da ta yi rashin nasara a tarihin kasar - ba wai rundunar soji ba. Manufarmu ita ce mu tabbatar da Isra’ila ta zama kasa mai hankali da ba ta kashe yara kanana a matsayin wasan nishadi ko manufarta.”

“Gwamnatin da ke maganar atom bam a Gaza ba gwamnatin Yahudawa ba ce, kuma ba ta masu rajin kafa kasar isra’ila ba ce.”

Jariran Gaza 14,000 na iya mutuwa a awanni 48

Shugaban Hukumar Ayyukan Jin Kai ta Majalisar Dinkin Duniya a ranar Talata ya yi gargadin cewa nan da awanni 48 jarirai 14,000 za su iya mutuwa a Gaza idan ba a bar manyan motoci dauke da kayan tallafi sun shiga yankunan Falasdinawa da ke Gaza ba.

Da yake magana da rediyon BBC, Tom Fletcher ya ce dubunnan motoci dauke da kayan taimako na kan iyaka, yana mai cewar kayan taimakon su hada da abincin jarirai.

Tsawon makonni 11 kenan Isra’ila ta hana a kai kayan agaji Gaza, kawai trloli tara ne suka shiga yankin a ranar Litinin, matakin da Sakatare Janar na MDD ya bayyana da digon ruwa a cikin teku.

Babu wani taimako da aka raba a Gaza, in ji MDD a ranar Talata, tana mai gargadin yiwuwar samun ibtila’in yunwa a Gaza.

Kakakin Majalisar Dinkin Duniya Stphen Dujarric ya ce a ranar Litinin an bar manyan motoci hudu dauke da abincin jarirai sun shiga Gaza, sai a ranar Talata da aka bar wasu dauke da magunguna, garin fulawa, da kayana abinci.

Tun Oktoban 2023 Isra’ila ke kai hari kan Gaza inda aka kashe kusan Falasdina 64,000, mafi ywan su mata d ayara kanana. Ana zargin an binne wasu 11,000 a karkashin buraguzan gini.

Amma kwararru na cewa mutanen da suka mutu sun haura 200,000.

Kotun Hukunta Manyan Laifuka ta Kasa da Kasa ta bayar da umarnin da a kamo Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu da Ministan Tsaron kasar Yoav Gallant saboda aikata laifukan yaki.

Isra’ila na kuma fuskantar tuhumar aikata kisan kiyashi a kotun kasa da kasa.

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us