Bukukuwan sallah a Gaza na daga cikin abubuwan da nake tunawa na zamanin ƙuruciyata. Mu kan tashi da duku-duku kafin fitowar rana, iskar safiya na ɗan kaɗawa kuma muna cike da zumuɗi.
Tun kafin mu cire kayan barci ni da 'yan’uwana mukan fara rungumar juna cikin murna, sannan sai mu fara shirin zuwa masallaci.
Mahaifiyarmu tana tashi tun da wuri, ta shirya sabbin farantai da kofuna, ta goge gida tare da gyara shi don tarar baƙin da ta san za su zo.
A waje, tituna suna fara cika da hayaniya — yara suna dariya yayin da suke wasa da tumaki, makwabta suna yi wa juna “Barka da Sallah” daga baranda, masu sayar da kaya suna fitar da kayan zaki da burodi sabon gashi.
Akwai jin dadi wanda yake yaduwa, wanda ba za a iya dakatarwa ba, ko da a wuri da ya saba da bakin ciki sosai. Duk da haka zuƙata kan cika da jin daɗi ko da kuwa a cikin yanayi na tsananin tsoro da fargaba.
A shekarun da suka gabata kafin yaƙin kisan kiyashi, a lokacin da ba zan iya kasancewa a wurin ba, nakan shiga cikin bukukuwan sallah. Zan kira dangina daga London in tambaye su ko suna shirin yin layya a wannan shekarar, da kuma son sanin wanda za su fara ziyarta.
Ba ma rasa tsegumi da hirarrakin yi a ko yaushe — mu ji waye da waye suka samu saɓani, kuma yaushe suka yi sulhu bayan yin faɗa a kan gahawar Larabawa da ake kira maqluba. Nakan aika kudi don taimakawa wajen sayen raguna, ina ji na a nesa, kuma ina ji na a kusa — kamar ina aika soyayya ta hanyar Western Union.
Iyali suna gyara tsoffin rauni, yara suna cike da farin ciki, kuma imani yana lullube komai da wata irin nutsuwa mai daraja.
Amma wannan shekarar, babu tumaki. Babu sabbin kwanuka. Babu ziyarce-ziyarce ko sulhu. Wannan shekarar, bana an yi Babbar Sallah a Gaza a tantuna a cikin yunwa.
Dangina ba ma magana a kan wanda za su ziyarta — sun mayar da hankali ne wajen neman ruwan sha mai tsabta da ɗan burodi.
Ba sa muhawara kan tumakin da za su yanka, domin a yanzu su ake yankawa.
Kanwata ta gaya mini cewa Kasuwar Sheikh Radwan — wadda ta kasance zuciyar birnin Gaza mai cike da hayaniya, inda take kai 'ya'yanta kowace Sallah don sayen kayan zaki da sabbin kaya — yanzu ta zama sansanin 'yan gudun hijira.
A tsakiyar birnin Gaza, shara tana ruɓewa a lokacin zafin bazara. Yara suna kuka don babu abinci. Babu kayan ado. Babu kayan zaƙi. Babu tumaki.
Wata ƙanwata da mijinta, wadanda duk sallar layya sai sun yi gashin nama don raba wa mabuƙata, a yanzu su ne mabukatan — gidansu da rayuwarsu sun lalace, an ƙwace mutuncinsu. Suna rayuwa a cikin tanti suna kalen ragowar burodi da ruwa.
A Ƙaramar Sallar da ta wuce, a gaban rusasshen masallacin kusa da gidanmu mahaifina ya yi sallar idi. A wannan sallar kam ma ba zai iya yin hakan ba — an kore shi daga unguwar gaba ɗaya.
Duk da haka, ya ƙi barin al'ada ta mutu. Ya shirya tare da makwabta don su taru a waje daya daga cikin tantuna su yi sallah, suna ƙoƙarin ceto wani ƙaramin yanayin Eid, don girmama abin da suka saba yi ko da a lokacin rikici.
Abu na ƙarshe da za su jura
Kuma duk da haka ba a bar imani ya yi rauni ba. Ko a cikin tarin ɓaraguzan ma suna yi wa juna murnar barka da sallah.
Mahaifiyata, wadda aka raba ta da gidanta take kuma cikin halin baƙin ciki har yanzu ba ta daina yin addu'o'inta na safe ba.
'Ya'yan yayyena da 'yan’uwana, ba su da ko takalman tafiya kuma duk sun rame saboda yunwa, amma har yanzu suna sanya duk wani tsaftataccen tufafi da za su iya samu, kamar dai girmama al'adar zai iya dawo da wani ɗan yanayin rayuwa.
Babu abin da ya rage don murna, amma suna nan da imaninsu ba don suna sa ran wata mu'ujiza ba, amma domin wannan shi ne abu na ƙarshe da ba a ƙwace musu ba.
A duniyar da suka rasa tsaro da abinci, har ma da damar yin makokin waɗanda suka rasu, imani ya zama wani makami mai sanya nutsuwa da tawali’u. Wata hanya ce ta cewa: muna nan har yanzu.
Na karanta wani rahoto da ya ambaci wani mahaifin yara hudu, Hussam Abu Amer, mai shekaru 37, yana zaune a kan tayil din da ya kone wanda ya kasance falo a birnin Gaza: “Na kasance mutum mai ciyarwa da kare iyali. Yanzu, ni mutum ne kawai da ke ba da labaran dare don karkatar da hankalin 'ya'yana daga ƙarar bama-bamai da jin yunwa.”
Kalmominsa suna yawo a cikin tantuna da ruɓaɓɓun gine-gine — uba na cike da damuwa da fargabar mai zai faru da iyalinsa.
Kuma wannan shi ne abin da ya rage. Bayan watanni na hare-hare marasa ƙarewa, ƙaura, da yunwa, a yanzu al'ummar Gaza ba neman abin murna suke ba — suna neman yadda za su yi rayuwa ne kawai.
A yanzu a Gaza ba a bikin salla — ba kamar yadda sauran duniya ke yi ba. Ba sa tashi da dariya, ko cin kayan zaki, ko sabbin kaya.
Rayuwar a yanzu ta koma ta shiru da tashin hayaƙi, da rashin abokan rayuwa. Amma har yanzu suna ƙoƙarin yin bikin sallah. Suna sallah da addu'o'icikin, suna rabon abinci duk da bai wadata ba, a cikin rungumar juna da ke ɗaukar lokaci mai tsawo don su samu nutsuwa.
A Gaza, bikin sallah ba murna ba ce yanzu. Tunawa ce, addu'a ce ga masu rai da matattu. Kuma wata irin shiru mai nuƙrƙusar zuciya: cewa ko da a cikin yaƙin kisan kiyashi, ruhin ɗan’adam, da al'adun soyayya da imani, suna ci gaba da kasancewa.
Domin a Gaza yau, mutane ba sa fatan samun kayan ado, ko murna, ko yanka tumaki. Suna fatan wani abu mafi sauƙi, mafi gaggawa. Suna addu'a don a tsagaita wuta. Suna so kawai a daina kashe-kashen.