Rahotanni daga Manchester United na cewa an cim ma yarjejeniyar ɗauko ɗan wasan ɗan asalin Kamaru, Bryan Mbeumo daga Brentford kan kuɗi fam miliyan £71 (dala miliyan $95.5m).
Bayan kwashe makonni ana tattaunawa, Mbeumo mai shekaru 26 ya zaɓi komawa United duk da ya samu tayi daga wasu ƙungiyoyin kamar Arsenal, Newcastle, da Tottenham.
Wannan na nufin ya zama ɗan wasa na uku da United ta sayo a kasuwar cinikin ‘yan wasa ta bazarar nan, a ƙoƙarinta na ƙarfafa tawagarta gabanin fara kakar baɗi ta 2025-26.
Daga jimillar kuɗin da ya kai fam miliyan £71, za a biya fam miliyan £65m kashi-kashi, da fam miliyan £6m ($8m) na bonos.
Sauran ‘yan wasan da Man U ta sayo zuwa yanzu su ne, Matheus Cunha da Diego Leon.
Bryan Mbeumo ya ci ƙwallaye 20 da taimakon cin ƙwallo 8 cikin wasanni 38 da ya buga a kakar bara.
Wannan ne ya sa sau biyu Brentford tana ƙin tayi daga United, har sai da aka cika farashin da suka gindaya masa.
A yanzu Mbeumo zai bar Brentford bayan buga jimillar wasanni 242, da cin ƙwallaye 70, da tallafin ƙwallo 51 tun sanda ya shiga ƙungiyar a 2019.