Ahmad Elnafaty ya tona bohol har biyar a gidansa da ke Kano cikin shekaru huɗu, amma babu ɗaya cikin bohol ɗin da ta iya ba da ruwa ko na mako ɗaya . Daga baya, kawai sai ya saduda.
Kamar gidaje da yawa a birnin na kasuwanci, iyalan Elnafaty yanzu sun koma siyan ruwa daga tankokin masu sayar da ruwa. A ko wane wata suna kashe naira 200,000, lamarin da iyalai da dama suka runguma a matsayin al’ada.
"Mugun rashin sa’a," kamar yadda Elnafaty ya shiada wa TRT Afrika Hausa, yayin da yake bayyana ƙoƙarinsa na samun ruwa daga ƙarƙashin ƙasa.
Abin da bai bayyana ba shi ne abin banmamakin ƙasar da koguna ke cika a duk lokacin da ƙasar Kamaru mai maƙwabtaka ta sako ruwa daga madatsar ruwar Lagdo, kuma miliyoyin ‘yan ƙasar ke fama da matsalar rashin nagartattun famfuna masu kawo ruwan sha.
Rashin isasshen ruwan shan ya haifar da wata masana’anta ta bayan fage. Wasu alƙalluman da hukumar UNICEF da Ma’aikatar Ruwa ta Tarayyar Nijeriya suka fitar a shekarar 2021 sun bayyana cewa daga cikin wuraren samar da ruwa miliyan 2.31 a faɗin ƙasar, kashi 75 cikin 100 na masu zaman kansu ne, kuma kashi 43 cikin 100 rijiyoyin bohol ne.
Matsaloli masu tono riba
Rashin isasshen ruwan sha a ƙasar da ta fi yawan mutane a nahiyar Afirka shi yake bai wa mutane da dama da ke sana’ar haƙar rijiyar bohol da sayar da injin bohol da ke janyo ruwa daga ƙasa da kuma masu gyara injin aikin yi. Kuma a wasu lokutan matsalar na hana yara zuwa makaranta.
"A jihar Kano , rijiyoyin bohol suna buƙatar su yi zurfin mita 30 zuwa 60 domin su iya samar da ruwa cikin kwanciyar hankali inda wasu ke buƙatar kai wa zurfin mita 250 ko kuma fiye da hakan," kamar yadda Lamir Safiyanu Madugu ya shiada wa TRT Afrika. "Matsakaicin zurfin rijiyar bohol a wajen da yake gangare ba ya wuce mita 20, yayin da mafi zurfin bohol ba ya wuce mita 60."
Haƙar rijiyar bohol na kaiwa kimanin naira miliyan 1,050,000 naira ($658), ba tare da kuɗin fetur na zuƙo ruwa daga ƙasa ba. A lokacin rani, lokacin da ruwa ke ƙasa-ƙasa sosai, Madugu na tona rijiyar bohol biyar zuwa goma a ko wane mako.
Masana da fitattun ‘yan Nijeriya suna gargaɗi game da matsalar da yawan tonon rijiyoyin bohol ka iya janyo wa muhalli. Tsohon Shugaban Ƙasa Olusegun Obasanjo na fargabar cewa bala’i na tafe, inda a lokacin da yake bayani game da yadda ake ta tonon bohol babu ƙaƙƙautawa a garinsa na Abeokuta da ke kudu maso yammacin Nigeria.
Kasawar tsari
Baya ga ma’aikatar tarayya, Nijeriya tana da ma’aikatun ruwa a kowace jiha cikin jihohi 36 na tarayyar da kuma babban birnin ƙasar Abuja, tare da hukumomin samar da ruwa da ke da alhakin samar da ruwan sha na famfo.
Ma’aikatar Samar da Ruwa da Tsaftace muhalli ta ƙasar ta bayyana a cikin watan Mayu cewa gwamnatin Nijeriya tare da wasu ƙungiyoyi na ƙasa da ƙasa ciki har da Bankin Bunƙasa Tattalin Arziƙin Afirka sun aiwatar da ayyukan samar da ruwa 565 cikin shekara biyu, inda ‘yan Nijeriya 451,000 suka ci gajiyarsa.
Dakta Zaharaddeen Garba, malami a fannin koyar da kimiyyar sinadirai a jami’ar Ahmadu Bello da ke Zaria, ya ce akwai buƙatar ƙara ƙoƙari wajen magance matsalar kuma ya alaƙanta matsalar da rashin isassun kayayyaki da rashin kula da kuma girman garuruwa da sauri.
"Bututun sun tsufa, kuma tsarin tura ruwa ba shi da inganci yayin da ikon tsaftace ruwa ya yi kaɗan," kamar yadda ya shaida wa TRT Afrika Hausa. "Wani dalilin kuma shi ne faɗaɗa yawan birane da kuma yawan mutane lamarin da ke matsa wa tsare-tsaren samar da ruwa da ake da su kuma yake janyo ƙaranci da kuma rashin daidaito."
Sauyin yanayi ya ƙara yamutsa matsalolin. Ƙarancin ruwan sama da kuma ƙarin bushewa na ƙara ɗumamar yanayi wadda ke tasiri kan ruwan tudu da na ƙarƙashin ƙasa.
Tattalin ruwan ambaliya
Masana sun yi imanin cewa Nijeriya za ta iya sauya fargabar ambaliya zuwa aminci na ruwan sha.
"Ƙaddamar da tsarin tattalin ruwan ambaliya da kuma tsarin ajiyar ruwa ɗaya ne daga cikin hanyoyin da Nijeriya za ta iya cin moriyar alfanun koguna da ke iya jnayo ambaliya domin samar da ruwan sha," in ji Dakta Garba.
"Wannan ya ƙunshi gina tafki da madatsun ruwa da kuma sauran kayayyakin aiki domin tarawa tare da adana ruwan ambaliya wanda za a iya tsaftacewa kuma a tura wa mutane. Nijeriya za ta iya amfani da irin fasaha na zamani irin wuraren tsaftace ruwa da ke yawo a kan ruwa da ko kuma ƙananan tsare-tsaren tsaftace ruwa domin tsaftace ruwan ambaliya."
Ta hanyar sarrafa ruwan ambaliya Nijeriya za ta iya sauya matsala zuwa kadara inda za ta iya tabbatar da aminci wajen samar da ruwan sha da kuma inganta ci-gaban tattalin arziki. Amma wannan na buƙatar tsari a hankali da zuba jari a samar da abubuwan more rayuwa da kuma haɗin kai tsakanin masu ruwa da tsaki.
"Bin hanyoyi da dama wajen magance matsalar na da muhimmanci wajen tabbatar da samun ruwan sha na din-din-din . Hanya ta farko ita ce zuba jari wajen inganta kayayyakin smar da ruwa, wanda ya haɗa da sabunta wuraren tsaftace ruwa da bututu da kuma tsare-tsaren raba ruwa," kamar yadda Dakta Garba ya bayyana.
Gwamnatocin jihohi ma suna kuma buƙatar inganta hukumomin gudanarwa na hukumomin samar da ruwan sha ta hanyar horaswa da amfani da fasaha da kuma bayyana gaskiya.
"Fifita matakan tattalin ruwa da kuma neman tsare-tsaren gudanarwa da zai iya taimakawa wajen rage ɓarna da kuma inganta amfani da ruwa," kamar yadda Dakta Garba ya bayyana wa TRT Afrika.
Yiwuwar mayar wa ‘yan kasuwa
Tun da buɗa fannin sadarwa ga ‘yan kasuwa tun shekarar 1999 ya bunƙasa tattalin arziki a ƙasar, wasu masu ruwa da tsaki suna goyon bayan irin wannan matakin na buɗa wa ‘yan kasuwa su shigo domin magance matsalar rashin ingancin fannonin da gwamnati ke tafiyarwa.
Amma masana na gargaɗin cewa kada a yi amfani da wannan a matsayin mafita kai tsaye.
"Gaskiya ne cire hannun gwamnati a fannin sadarwa a Nijeriya ya kawo muhimmin ci-gaba a fannin. Sai dai kuma, aiwatar da irin wannan matakin a hukumomin samar da ruwan sha na jihohi ba zai yiwu kai tsaye haka kawai ba. Wannan na da sarƙaƙiya kaɗan," in ji Dakta Garba.
Ya yi imanin cewa mayar da hukumomin samar da ruwa na jihohi hannun ‘yan kasuwa ka iya ƙara inganci a ayyukansu, amma matsalar sauƙi ka iya zama ƙalubale ga mutane musamman a gidajen marasa galihu.
Dakta Garba ya ba da shawarar bai wa ‘yan kasuwa damar taka rawa wajen samar da kayayyakin samar da ruwa da kuma yi wa mutane hidima, yayin da hukumomi za su yi ta sa ido "domin tabbatar da cewa kowa ya samu [ruwan sha] cikin sauƙi”.
Masu amfani da ruwa kamar Elnafaty, wanda a halin yanzu suna siyan ruwa daga ‘yan ga-ruwa ko kuma suna kashe kuɗi wajen siyan man fetu na janyo ruwa, ba za su ƙi biyan kuɗi ba idan za su sami ruwa daga famfo a ko da yaushe.