KASUWANCI
3 minti karatu
Turkiyya da Libya sun kulla yarjejeniyar hakar ma’adanai, samar da makamashi da ababen more rayuwa
Turkiyya kasa ce mai karfin gaske duba ga tattalin arziki da makamashi, in ji shugaban kamfanin Emaar Libya Holding.
Turkiyya da Libya sun kulla yarjejeniyar hakar ma’adanai, samar da makamashi da ababen more rayuwa
Hukumar DEİK na sanya hannu / AA
18 Yuli 2025

Turkiyya da Libya sun sanya hannu kan wata yarjejeniya a ranar Alhamis don hada kai wajen hakar ma’adanai, samar da makamashi da ababen more rayuwa.

Hukumar Hulda da Tattalin Arzikin Kasashen Waje ta Turkiyya (DEIK), Majalisar Harkokin Kasuwancin Turkiyya-Libya, Kamfanin Ma'adinai na Libya, Babbar Hukumar Kula da Baje-Koli da Taro ta Libya da Kamfanin Emaar Libya Holding sun sanya hannu kan yarjejeniyar fahimtar juna, wanda kuma ke da manufar kara yawan kasuwanci tsakanin kasashen biyu a fannoni uku.

Murtaza Karanfil, shugaban kwamitin kasuwanci na Turkiyya da Libya a DEIK, da Fouad Al-Awwam, shugaban kamfanin Emaar Libya Holding ne suka sanya hannu kan yarjejeniyar.

A jawabin da ya yi, Karanfil ya ce alakar Turkiyya da Libya ta samo asali ne tun tarihi mai tsayi.

Da yake lura da cewa an sanya hannu kan yarjejeniyar da Emaar Holding, wanda ke da kamfanoni 30 a karkashinsa, kuma yake gudanar da ayyuka a bangarori da dama, musamman a fannin masana’antu, ya ce kamfani ne da ya zuba jari da dama tare da bude wuraren kasuwanci musamman a gabashi da kudancin Libya.

"A matsayin mu na 'yan kasuwar Turkiyya, duk da cewa muna aiki tare da dukkanin Libya, amma hadin gwiwar da za mu yi da Emaar Holding don bunkasa dangantaka da yankin gabashin kasar zai samar mana da gagarumar nasara."

Kara yawan kasuwanci

Da yake zantawa da kamfanin dillancin labarai na Anadolu, Karanfil ya ce kayayyakin da Turkiyya ke fitarwa zuwa Libiya sun ragu zuwa dala biliyan 2.5 sakamakon rashin zaman lafiya a kasar da ke arewacin Afirka bayan shekarar 2014, wanda ya rage a wannan matakin kusan shekaru 10 da suka gabata, kuma jimillar kasuwancin ya kai dala biliyan 4 a halin yanzu.

Ya ce yarjejeniyar na da manufar bunkasa hadin gwiwa da gabashin Libya, inda ya kara da cewa "muna son kara yawan kasuwancin."

Da yake jan hankali kan dimbin tarin ma'adanan da aka gano a kudancin Libya a shekarun baya-bayan nan, Karanfil ya ce: "Mun bukaci su samar mana da taswirorin ma'adanan, musamman na kudancin kasar, da kuma sanar da mu wuraren da suke son ba da fifiko ga zuba jari da hadin gwiwa."

"Saboda haka, muna da manufar kawo fasahar ayyukan hakar ma'adanai na Turkiyya zuwa gabashin Libya ta hanyar shirya taron baki da baki tare da kamfanoninmu, idan hakan ya zama tilas."

Karin kamfanoni a bangaren makamashi

Karanfil ya yi nuni da cewa yankin kudancin Libya na da tarin ma'adanan masu yawa da ke jan hankalin kasashe da dama, Karanfil ya ce: "A yau, kamfanonin Turkiyya shida ne kawai suka yi rajista da kungiyar ma'adanai ta Libya."

"Muna son kara yawan wannan adadi kuma mu yi aiki tare da Libya, musamman a fannin makamashi."

Ya kara da cewa Libya kofa ce ta shiga Afirka, kuma hanyar fita daga Afirka zuwa sauran sassan duniya.

Al-Awwam ya kuma ce, Turkiyya kasa ce mai karfi ta fuskar tattalin arziki da makamashi.

"A matsayin Emaar Holding, za mu sanya hannu kan yarjejeniyoyin da Turkiyya a wadannan bangarorin," in ji shi.

"Haka kuma, kokarinmu na ci gaba da kai kasuwannin Turkiyya zuwa Libya, da kafa wata kasuwa mai dore wa ta kayayyakin Turkiyya, da kuma saukaka tsarin rarraba su."

Yi somin-taɓin a TRT Global. Bari mu ji ra'ayoyinku!
Contact us