11 Yuni 2025
Za ka iya buɗe wayarka don duba saƙo, amma sai ka bige wajen kallon bidiyo da hotuna tare da karanta sakonnin da aka wallafa har zuwa lokacin da za ka shafe awanni da dama ba tare da ka sani ba. Wataƙila a yanzu haka kana duba shafukan kafofin ne a yayin da kake sauraron wannan shirin. Amma ka taɓa tunanin yadda wannan ɗabi'a take shafar lafiyar jikinka? Muna yawan jin batun illar kafofin soshiyal midiya ga lafiyar kwakwalwarmu. Suna iya jefa mutane da dama cikin damuwa tare da takura su wajen zabar rayuwa mai cike da rudu ta jin dadi.