Kasar Sudan ta shigar da karar ƙasar kan Hadaddiyar Daular Larabawa a kotun ICJ tana mai cewa kasar ta yankin Gulf tana da hannu a kisan kiyashin da ake zargin tana goyon bayan rundunar sojojin kasar Sudan ta Rapid Support Forces da yi, kamar yadda Kotun Ƙasa da Ƙasa ta sanar a ranar Alhamis.
Khartoum ta ce UAE tana da hannu a kisan kiyashin da ake yi wa al’ummar Masalit a Sudan, ta hanyar jagoranci da bayar da tallafin kudi da siyasa, da kuma soji ga 'yan tawayen RSF," in ji ICJ a cikin wata sanarwa.
"Hadaddiyar Daular Larabawa ce ke rura wutar tawaye tare da goyon bayan mayakan da suka aikata laifin kisan kiyashi a yammacin Darfur," in ji sanarwar da Sudan ta gabatar a gaban kotun.
Hadaddiyar Daular Larabawa, wacce ta sha musanta goyon bayan kungiyar ta RSF, ta yi watsi da ƙarar a matsayin "neman suna" kuma ta ce za ta yi kokarin watsi da hakan.
UAE ta ce ƙarar 'ba ta da tushe'
Shari'ar "ba wani abu ba ne illa neman suna da aka yi da nufin karkatar da hankali," in ji wani jami'in Hadaddiyar Daular Larabawa a cikin wata sanarwa da ya aike wa AFP, yana mai cewa: "UAE za ta nemi a yi watsi da wannan ƙara maras tushe nan take."
Kusan shekaru biyu ke na RSF da rundunar sojin Sudan sun gwabza yakin da ya kashe dubban mutane tare da raba wasu fiye da miliyan 12 da muhallansu. An ayyana cewa sassan kasar na fama da yunwa kuma mai yuwuwa ta yadu.
Sudan ta yi kira ga Kotun ICJ da ke yanke hukunci a tsakanin kasashe, da ta ba da umarnin gaggawa - "matakan wucin gadi" a cikin sharuddan kotun - don tilasta wa UAE ta biya diyya, da sauran buƙatun.
"Dole ne Hadaddiyar Daular Larabawa ta biya cikakkiyar diyya kan raunukan da ta jawo sakamaon ayyukanta na ba daidai ba, gami da biyan diyya ga wadanda yaƙin ya shafa," in ji sanarwar Sudan.
Rashin ikon aiwatarwa
Hukunce-hukuncen kotun ICJ suna aiki bisa doka amma kotun ba ta da ikon aiwatar da su.
Misali, umarnin da ta bai wa Rasha na dakatar da farmakin da take kai wa Ukraine makonni kadan bayan mamayar - bai yi wani tasiri ba.
Amma Khartoum ta bukaci kotun da ta gaggauta daukar matakin "domin tabbatar da samar da kariya cikin gaggawa da cikakkiyar kariya ga fararen hular Sudan da ke cikin mawuyacin hali da kuma hadarin ci gaba da aiwatar da kisan ƙare dangi."
Sanarwar ta Sudan ta zargi kungiyar RSF da "kisan kare dangi, da satar dukiya, fyade, tilasta wa mutane barin muhallansu, yin kutse, lalata kadarorin jama'a, da kuma take hakkin dan’adam."
Sudan ta ce RSF na karbar makamai daga UAE.
Ta ƙara da cewa wadannan ayyukan "an yi su ne ta hanyar tallafin kai tsaye da Hadaddiyar Daular Larabawa ke bai wa 'yan tawayen RSF da kungiyoyin sa kai masu alaka."
Sudan ta yi zargin cewa Hadaddiyar Daular Larabawa tana keta hakkinta a karkashin yarjejeniyar kisan kare dangi ta Majalisar Dinkin Duniya ta 1948 "ta hanyar yunkurin aikata kisan kiyashi, hada baki da tayar da kayar baya, da hannu wajen kisan kare dangi, da kasa hanawa da hukunta kisan kiyashi."
"Zarge-zargen da wakilin SAF ya gabatar a kotun ICJ ba shi da wani tushe na shari'a ko na gaskiya, wanda ke wakiltar wani yunƙuri na kawar da kai daga wannan mummunan yaƙi," in ji jami'in UAE.
A watan Yuni, jakadan Majalisar Dinkin Duniya na Sudan Al-Harith Idriss al-Harith ya zargi Hadaddiyar Daular Larabawa da haddasa rikici a kasarsa, yana mai cewa "Emirates na tallafa wa RSF da makamai".