Kamfanin man fetur na Nijeriya NNPCL ya ce ya shirya ƙara yawan gidajen mansa zuwa 2,000 kafin ƙarshen 2025.
Shugaban ɓangaren watsa labarai na kamfanin, Mista Olufemi Soneye ne ya tabbatar da hakan a yayin wani taron ƙara wa juna sani wanda aka shirya wa ma’aikatan gudanarwa na Majalisar Tarayyar Nijeriya.
Mista Soneye ya bayyana cewa domin bunƙasa ayyukan NNPCL a ƙasar, kamfanin ya ƙara adadin gidajen mansa a Nijeriya daga 897 a bara zuwa fiye da 1,000 bayan samun ƙarin gidajen mai a makon da ya gabata.
Ya bayyana cewa kamfanin na NNPCL wanda shi ne mafi girma a Afirka na shirin ƙara adadin gidajen mansa zuwa 2,000 kafin ƙarshen shekarar 2025.
Jaridar The Nation a Nijeriya ta ruwaito Mista Soneye yana cewa duka matatun mai na NNPCL na aiki banda na Fatakwal da Kaduna waɗanda ya bayar da tabbacin cewa su ma za su fara aiki kafin ƙarshen 2025.
Soneye ya bayyana cewa tun bayan da aka sake buɗe matatun da aka gyara, har yanzu ba su tsaya ba suna aiki.
Tun bayan cire tallafin mai a Nijeriya, ‘yan ƙasar na kokawa game da tsadar fetur a ƙasar.
Sai dai kamfanin na NNPCL na cewa yana ɗaukar matakai waɗanda za su kai ga samun sauƙi.