Afirka
2 minti karatu
Nijar na son karkata ga tauraron ɗan'adam domin samar da intanet a ƙasar
Rashin samun intanet a wasu sassan ƙasar ya samo asali ne sakamakon ƙarancin zuba jari da kuma lalata turakun samar da sabis da ƙungiyoyin ‘yan bindiga ke yi a ƙasar, kamar yadda hukumar da ke sa ido kan sadarwa ta Nijar ARCEP ta bayyana.
Nijar na son karkata ga tauraron ɗan'adam domin samar da intanet a ƙasar
Akwai sassa da dama na Nijar da ke fama da matsalar intanet
2 de março de 2025

Ƙasa da kashi ɗaya bisa uku na faɗin kasar Nijar ne ke da intanet, wanda a halin yanzu ya sa ƙasar da ke Yammacin Afirka ke ƙoƙarin mayar da hankalinta kan amfani da tauraron ɗan adam domin cike giɓin intanet ɗin a karkara.

Rashin samun intanet ɗin a wasu sassan ƙasar ya samo asali ne sakamakon ƙarancin zuba jari da kuma lalata turakun samar da sabis da ƙungiyoyin ‘yan bindiga ke yi a ƙasar, kamar yadda hukumar da ke sa ido kan sadarwa ta Nijar ARCEP ta bayyana.

A watan Nuwamba ne dai mahukuntan kasar ta Nijar suka ba da kwangilar shekaru biyar ga hamshaƙin attajirin nan na Amurka Elon Musk mai kamfanin Starlink domin samar da intanet mai ƙarfi a faɗin ƙasar da ke yankin Sahel.

Nijar na daga cikin ƙasashe 15 na Afirka da suka amince da amfani da intanet ɗin Starlink a yankunansu.

Tsadar samun intanet

“Muhimman wurare da ke tafiyar da ci gaban tattalin arziki waɗanda suka haɗa da bankuna da asibitoci da makarantu da makamashi da ɓangaren noma duk sun dogara ne kan intanet,” in ji masanin tattalin arziƙi Ibrahim Adamou Louche.

Ministan watsa labarai na Nijar Sidi Ahmed Raliou ya yi hasashen cewa wannan yunƙurin zai samar da intanet ga kusan “kaso 80 zuwa 100” na Nijar – murabba’in kilomita 1,267 wanda akasari sahara ce.

Ana ganin wannan yarjejeniyar za ta zama wata babbar riba ga tattalin arziƙin kamfanin na Amurka.

A ƙasar da kusan kaso 50 cikin 100 na jama’ar ƙasar na rayuwa ƙasa da dala ɗaya a rana kamar yadda Bankin Duniya ya bayyana, jama’ar da ke son amfani da intanet dole ne su biya tsakanin CFA 260,000 zuwa 400,000 ($414 da $637) domin samar da kayayyakin amfani na kamfanin na Starlink.

 

 

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us