Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce Musulmai waɗanda suka kai rubu’in yawan jama’ar duniya dole su samu wakilci a tsarin tafiyar da duniya kamar yadda ya dace su samu.
Erdogan ya ce, “Samun ƙasar Musulunci mai ikon hawa kujerar-na-ƙi a Kwamitin Tsaro na Majalisar Ɗinkin Duniya wajibi ne, maimakon buƙata.”
“Gwagwarmayarmu, bisa ƙa’idar cewa "duniya ta fi ƙasashe biyar kawai," na da manufar cim ma wani tsari da ya fi bai wa kowa haƙƙinsa domin maye gurbin tsarin duniya da ke sa matsaloli su dawwama," in ji shi, yana mai ƙarawa da cewa: “Lokaci ya riga ya yi da tsarin tafiyar da duniya zai sauya ta yadda duniya ke sauyawa.”
"Isra’ila ba za ta samu kwanciyar hankalin da take nema ba idan ba a kafa ƙasar Falasɗinu mai cin gashin kanta bisa kan iyakokin shekarar 1967 ba,” kamar yadda Erdogan ya yi gargaɗi.
"Baya ga kirar da suke na mamaye gaɓar yamma da kogin Jordan, ministocin gwamnatin Isra’ila suna wasa da wuta da hankorar tsokana da suke yi wa masallacin Ƙudus," in ji shi, yana mai jadda cewa masallacin ƙudus ɗin mai cike da tarihi wuri ne da Turkiyya ba ta lamuntar wasa da shi.
Tsaron Turai ba ta iya kasancewa ba tare da Turkiyya be
Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya ce ba za a iya tunanin tsaron Turai babu Turkiyya ba.
Turkiyya na ganin shigarta ƙungiyar Tarayyar Turai a matsayin wata " dabara da ta bai wa fifiko," saboda ita “wani ɓangare ne da ba za a iya raba ta da Turai ba," in ji Shugaba Erdogan a wani jawabin da ya yi wa jakadun ƙasashen waje da ke aiki a babban birnin ƙasar Ankara ranar Litinin.
"Yana daɗa zama abin da ba zai yiwu ba Turai ta ci gaba da kasancewa mai-faɗa-a-ji a duniya ba tare da Turkiyya ta kama matsayin da ta cancanta ba," in ji shi a lokacin cin abincin buɗe-baki na azumin watan Ramadan