Yayin da a yau Talata za a fara zagayen ‘yan-16 na gasar Zakarun Turai, Arsenal za ta kara da PSV Eindhoven, Real Madrid da Atletico Madrid, Borussia Dortmund da Lille, sai kuma Club Brugge da Aston Villa.
Kocin Arsenal, Mikel Arteta ya ayyana cewa a wannan shekarar, yana da ƙwarin gwiwar cewa Arsenal tana da abin da ake buƙata don lashe kofin Zakarun Turai saboda ɗorewar tagomashinsu.
Arsenal ta samu gurbi a matakin ‘yan-16 na gasar, inda ta ƙare zagayen rukuni a mataki na uku a tebur. A wancan matakin, an ci ƙungiyar ƙwallaye uku ne kacal, a wasanni takwas, wanda shi ne na biyu a ƙanƙanta.
Da yake magana da manema labari gabanin wasan da za a yi a maraicen yau, kocin ya ce, "Wannan shekarar mun fi samun ɗorewar tagomashi. Mun ci ƙwallaye da dama kuma kusan ba a ci mu ba. Ƙwallo uku kawai aka ci mu, mafi ƙanƙanta kan yadda aka saba gani, wanda abu ne mai kyau."
Arteta ya ce, “Muna da duk abin da ake buƙata [don lashe kofin Zakarun Turai]. Kuma wannan shi ne abin da ƙungiyarmu ta riga ta yi. Yanzu dole mu ci gaba da yin hakan. Idan ka duba ƙungiyoyi da suka yi nasara, ƙarfin su a tsaron baya yana da muhimmanci.
Koma-baya a Firimiya
Ana kallo abin da kocin ya yi na cika-baki kan fatan lashe kofin Turai a matsayin saddaƙarwar cewa kofin Firimiya ya fara yi musu nisa.
A gasar Firimiya a gida Ingila, Arsenal na mataki na biyu, duk da dai jagabar gasar Liverpool ta kere mata da tazarar maki 13.
Ko a makon jiya, Arsenal ta yi canjaras da Nottingham Forest da 0-0, wanda ya janyo musu asarar maki biyu daga ukun da suke da damar samu daga wasan.