Afirka
2 minti karatu
Shugaban Guinea-Bissau ya yi barazanar korar wakilan ECOWAS daga ƙasar, in ji ƙungiyar
Embalo, wanda ya jagoranci ECOWAS daga tsakiyar shekarar 2022 zuwa tsakiyar shekarar 2023, ya bayyana a ranar 23 ga watan Fabrairu cewa ba za a yi zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisu ba sai ranar 30 ga watan Nuwamba.
Shugaban Guinea-Bissau ya yi barazanar korar wakilan ECOWAS daga ƙasar, in ji ƙungiyar
Ranar Laraba, Embalo ya ziyarci Rasha domin tattaunawa da Shugaban Rasha Vladimir Putin.
March 3, 2025

Shugaban Guinea-Bissau, Umaro Sissoco Embalo, ya yi barazanar korar wakilan da ƙungiyar raya tattalin arzikin Yammacin Afirka (ECOWAS) ta tura ƙasarsa, in ji sanarwar da ƙungiyar ta fitar ranar Lahadi.

Ce-ce-ku-ce kan ko wa’adin mulkin Embalo, wanda ya fara aiki a shekarar 2020, ya kamata a ce ya ƙare yana tayar da hankali, lamarin da ke barazanar rura wutar rikici a ƙasar da ke da tarihin juyin-mulki.

‘Yan adawa a ƙaramar ƙasar ta Yammacin Afirka sun ce ya kamata a ce wa’adin mulkin Embalo ya ƙare a makon da ya gabata, yayin da Kotun Ƙolin ƙasar ta ce zai ƙare ne a ranar 4 ga watan Satumba.

Embalo, wanda ya jagoranci ECOWAS daga tsakiyar shekarar 2022 zuwa tsakiyar shekarar 2023, ya bayyana a ranar 23 ga watan Fabrairu cewa ba za a yi zaɓen shugaban ƙasa da na ‘yan majalisu ba har sai ranar 30 ga watan Nuwamba.

A wata sanarwar da ta fitar ranar Lahadi, ECOWAS ta ce ta tura wakilai ne daga ranar 21 zuwa 28 ga watan Fabrairu tare da ofishin Majalisar Ɗinkin Duniya na Yammacin Afirka da Sahel (UNOWAS) domin cim ma yarjejeniya game da yadda za a gudanar da zaɓe a wannan shekarar.

Amma ta ƙara da cewa: "Wakilan sun bar Bissau da sanyin safiyar ranar 1 ga watan Maris, bayan barazanar da Mai Girma Umaro Sissoco Embalo ya yi na korarsu."

Ranar Laraba, Embalo ya ziyarci Rasha domin tattaunawa da Shugaba Vladimir Putin.

 Guinea-Bissau dai ƙasa ce renon Portugal kuma ta samu ‘yancin kanta ne a shekarar 1974.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us