Siyasa
3 minti karatu
Majalisar Dattijan Nijeriya ta dakatar da Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida
Majalisar Dattijan Nijeriya ta kuma yanke shawarar dakatar da albashi da alawus-alawus na Mrs Akpoti-Uduaghan yayin da za a janye dukkan mataimakanta na tsaro a lokacin dakatarwar.
Majalisar Dattijan Nijeriya ta dakatar da Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida
Majalisar Dattijan Nijeriya ta dakatar da Natasha Apoti-Uduaghan na tsawon watanni shida
5 saat əvvəl

Majalisar Dattijan Nijeriya a ranar Alhamis ta dakatar da sanata mai wakiltar Kogi ta Tsakiya, Natasha Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida bisa zarginta da rashin ɗa’a da kuma ƙin bin tsarin zama a yayin wani zaman majalisar na ranar 20 ga watan Fabrairu.

Babban zauren majalisar, ya ce idan Misis Akpoti-Uduaghan ta miƙa takardar neman afuwa a rubuce, shugabannin majalisar na iya duba yiwuwar ɗage dakatarwar kafin wa'adin watanni shidan ya cika.

Shugaban Majalisar Dattawa, Godswill Akpabio, ya sanar da dakatar da Misis Akpoti-Uduaghan bayan da akasarin Sanatoci suka mara masa baya a Zauren Majalisar.

Rikicin ya fara ne lokacin da Misis Akpoti-Uduaghan ta ƙi amincewa da zama a sabon wajen zamanta, inda ta ce an yi hakan ne ba tare da amincewarta ba kuma ta yi imanin cewa matakin ya saɓa da alfarmar ofishinta.

Kwamitin ɗa’a

Daga nan ne aka miƙa batun ga kwamitin majalisar dattawa kan ɗa’a, gata, da ƙararrakin jama’a, karkashin jagorancin Neda Imasuen (LP, Edo South).

Da yake gabatar da rahoton kwamitin, Mista Imasuen ya bayyana cewa, kwamitin ya sake duba koke-koken da ake yi a kan Sanata Akpoti-Uduaghan, tare da yin la’akari da kundin tsarin mulkin Nijeriya da dokokin majalisar dattawa, da kuma ƙa’idojin daidaito da adalci.

Mista Imasuen ya ce an gayyaci Mrs Akpoti-Uduaghan da shugaban kwamitin majalisar dattijai kan harkokin yada labarai da wayar da kan jama’a, Yemi Adaramodu domin gabatar da matsayinsu. Sai dai yayin da Mista Adaramodu ya mutunta gayyatar, Misis Akpoti-Uduaghan ta ƙi bayyana, matakin da kwamitin ya dauka a matsayin rashin mutuntawa.

Dangane da zargin cin zarafi da ake yi wa Mista Akpabio, shugaban kwamitin ya ci gaba da cewa ya yi watsi da ƙarar ne saboda ta saɓa wa dokokin majalisar dattijai, saboda ita ce ta sanya mata hannu.

Shawarar da kwamitin ya yanke

Bayan binciken kwamitin, Mista Imasuen ya ba da shawarar dakatar da Misis Akpoti-Uduaghan na tsawon watanni shida daga ranar 6 ga Maris tare da ƙarin wasu hukuncin, gami da janye dukkan mataimakanta na tsaro.

Shugaban kwamitin ya kuma ba da shawarar a rufe ofishin Misis Akpoti-Uduaghan a cikin Majalisar Dokokin kasar tare da dakatar da albashi da alawus-alawus ɗinta.

Ya kuma bayar da shawarar a hana Sanatar ta Kogi wakilcin Majalisar Dokokin kasar nan a cikin gida da waje a tsawon lokacin dakatar da ita.

Daga nan sai shugaban majalisar dattijan ya gabatar da shawarar a kaɗa ƙuri’a, kuma yawancin ‘yan majalisar sun goyi bayan dakatarwar.

An saka jami’an tsaron majalisar sun fitar da Mrs Akpoti-Uduaghan daga cikin zauren a yayin da take ihun cewa “wannan rashin adalcin ba zai tabbata ba.”

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us