Ministan harkokin cikin gida na Libya Emad Trabelsi ya bukaci tawagar Majalisar Dinkin Duniya a Libya (UNSMIL) da ta tallafa wa shirin komawar ‘yan gudun hijira da ‘yan ci-rani da suka nuna sha’awar koma wa kasashensu na asali daga Libya.
Bukatar hakan ta zo ne a yayin taron da Trabelsi ya yi da wakiliyar MDD ta musamman a Libya Hanna Tetteh da tawagarta wadanda suka kawo ziyara hedkwatar ma’aikatar harkokin cikin gida na kasar da ke birnin Tripoli a ranar Laraba, a cewar sanarwar da ma’aikatar ta fitar.
Sanarwar ta ce taron ya tattauna batutuwan da suka shafi tsaro daban-daban da karin bayanai game da ayyukan ma’aikatar, da kuma dabarun tsaro da nasarorin da ta samu a kasa.
A yayin taron, Trabelsi ya bayyana mumunan illar tasirin yadda ake hijira ba bisa ka'ida ba a kan Libya da kasashen Mediterranean tare da jaddada muhimmancin goyon bayan Majalisar Dinkin Duniya ga kokarin ma'aikatar wajen aiwatar da shirin komawar ‘yan gudun hijirar da ke son komawa gida bisa ga son ransu.
Hanyar hamada
A watan Yulin 2024, Trabelsi ya kiyasta cewa yawan ‘yan gudun hijira a Libya ya wuce mutum miliyan 3, inda ake samun kwararar bakin haure 90,000 zuwa 120,000 da ke shiga kasar duk wata ta hanyar hamada.
Baya ga wannan shiri na Libya, Hukumar Kula da ‘Yan gudun hijira ta Duniya (IOM) ita ma tana gudanar da shirin mayar da ‘yan gudun hijirar da ke son koma wa gida bisa ga kashin kansu.
Tun daga shekarar 2015, hukumar IOM ta taimaka wajen mayar da ‘yan gudun hijira kusan 80,000 daga Libya, a cewar kididdigar Majalisar Dinkin Duniya.
Kasar Libya dai na ci gaba da fuskantar kalubalen ‘yan ci-rani, inda kasashen Tarayyar Turai da ke gabar tekun Mediterrenean ke nuna damuwarsu kan yadda bakin haure ke kwarara zuwa gabar tekunsu.
A halin da ake ciki kuma, mahukuntan Libya sun jaddada cewa, kasar ta kansance wuri da ake ratsawa ta cikinta ba wai kasa ta asali ba da ‘yan ci-ranin ke tasowa ba, suna masu zargin kasashen Turai da yin sakaci da rawar da suke takawa wajen shawo kan lamarin.