An yi bikin ɗaga tutar Ƙungiyar Ƙasashen Sahel (AES) a hukumance Fadar Shugaban Nijar, a wata alama ta ƙarfafa hadin gwiwa tsakanin Nijar da Mali da Burkina Faso.
Gidan talabijin na Janhuriyar Nijar RTN ya ce an yi bikin ne a yau Litinin 3 ga watan Maris din 2023, “ranar da ta zama wani lokaci mai cike da tarihi ga yankin Sahel.”
RTN ta ce wannan tuta ta ƙunshi ƙudurorin ƙasashen na samar da ɗiyauci da zaman lafiya da cigaban yankinsu.
“Wannan sabuwar alama ta ƙungiyarmu a yanzu tana tsaye da alfahari, tana ɗauke da burin miliyoyin al'ummar Sahel zuwa makoma mai daraja da wadata,” in ji RTN.
A ranar 29 ga Janairun 2025 ne ƙasashen Mali da Burkina Faso da Nijar - da a yanzu suka hade karkashin Kawancen Kasashen Sahel (AES) - suka sanar a hukumance sun fice daga Kungiyar Rayar Tattalin Arzikin Kasashen Yammacin Afirka (ECOWAS), wanda hakan ya zama babban sauyi a fagen siyasar yankin.
Wannan ballewa ta bazata na bayyana al'amarin da ya fi na rikicin diflomasiyya girma, na bayyana tsananin damuwa game da kawancen tsaro da dogaron tattalin arziki, da 'yancin kan siyasa.
Ko a ƙarshen watan da ya gabata ma Shugaban Sojin Sama na Nijeriya ya ce ficewar ƙasashen Nijar da Mali da Burkina Faso daga ECOWAS na shafar aikinsu na haɗin gwiwar soji a yankin Sahel inda ya ce a halin yanzu duk wani nauyi ya rataya a wuyan sojojin Nijeriya.
Sahel Alliance
Sahel Alliance ko Ƙungiyar Ƙawancen Sahel, ko kuma AES a taƙaice ƙungiya ce ta ƙasashe uku da ke Yammacin Afirka da a yanzu haka suke ƙarƙashin mulkin soja, wadanda kuma suka fice daga Ƙungiyar ECOWAS.
Mambobin AES su ne Burkina Faso da Mali da kuma Jamhuriyar Nijar.
Har yanzu dai wannan ƙungiya sabuwa ce, domin duk a cikin wannan shekara ta 2025 ne AES ta ƙaddamar da tutarta, da sabon fasfo da ma rundunarta ta haɗin gwiwa domin yaƙar ‘yan ta’adda da suka addabi yankin.