Shugaban mulkin soja na Gabon Janar Brice Oligui Nguema, wanda ya jagoranci juyin mulkin 2023 da ya kawo karshen mulkin iyalen gidan Bango na shekara 55, ya sanar ranar Litinin cewa zai yi takara a zaben shugaba kasa da za a yi a watan Afrilu.
Oligui ya yi alkawarin mika mulki ga farar hula bayan wa’adin rikon kwarya sakamakon juyin mulkin da aka yi wa Ali Bongo Ondimba a Agustan 2023.
Wata sabuwar dokar zabe da majalisar mika mulki ta amince da ita a karshen Janairu ta ba da dama ga sojoji da alkalai su tsaya takara.
‘Farfadowa daga mawuyacin hali’
"Bayan kyakkayawan nazari da kuma kiraye-kirayenku, na yanke shawarar yin takara a zaben shugaban kasa na ranar 12 ga watan Afrilu,” a cewar Oligui a wani jawabi da ya gabatar a babban birnin kasar, Libreville.
Oligui, wanda ya cika shekaru 50 a ranar Litinin, ya ce fatansa ga ‘yar karamar kasar mai arzikin man fetur shi ne “farfado da ita daga mawuyacin halin da take ciki”.