Majalisar Dokokin ECOWAS ta kafa wani kwamiti na musamman wanda zai sake tattaunawa da shugabannin ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar waɗanda suka ɓalle daga ƙungiyar.
Shugaban Majalisar Dattawan Nijeriya Sanata Barau Jibrin wanda mamba ne a majalisar ta ECOWAS ya tabbatar da hakan a yayin wata tattaunawa da gidan rediyon Faransa a Nijeriya.
Ya bayyana cewa an cim ma wannan matsayar ne bayan taron Majalisar ta ECOWAS wanda aka gudanar a birnin Legas na Nijeriya.
Barau ya ce bukatar wannan sabon kwamitin shi ne gudanar da tattaunawa ta fahimta a tsakanin shugabannin waɗannan kasashe da zummar janyo hankalin su a kan muhimmancin ci gaba da zama a cikin ECOWAS, idan aka yi la'akari da tasirin zamantakewar da ke tsakanin jama’ar su wajen aiki tare, ganin irin dogon lokacin da aka kwashe ana aiki tare.
Shugabar Majalisar Dokokin ECOWAS Hadja Memounatou Ibrahima ta jaddada buƙatar kafa wannan kwamitin inda ta ce hakan zai magance matsalolin da ake fuskanta a faɗin yankin
Haka kuma baya ga batun magance matsalolin siyasa a ƙasashen Yammacin Afirka, ana sa ran kuma zai daƙile ficewar ƙarin ƙasashen yankin daga ƙungiyar ECOWAS.
A ranar 29 ga Janairun 2025, ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar - da a yanzu suka hade ƙarƙashin Kawancen Kasashen Sahel (AES) - suka sanar a hukumance sun fice daga ECOWAS.
Sai dai duk da ficewar ƙasashen daga ƙungiyar, babu shinge tsakanin ECOWAS da AES ta ɓangaren sufuri da cinikayya inda ‘yan ƙasashen ke mu’amala ba tare da tsangwama ba.
Haka kuma ECOWAS ta bayyana cewa ƙofarta a buɗe take ga ƙasashen AES idan za su koma.