An gudanar jana’izar sojojin Nijar 11 a ranar Asabar bayan wani harin kwanton-ɓauna da ɓarayin daji suka kai kan sojojin.
Rahotanni daga Nijar ɗin sun ce an kashe sojojin ne a ranar Juma’a a yankin Ekade Malane da ke yankin Agadez a kusa da iyakar Nijar da Aljeriya.
Ƙungiyar ta’addanci ta JNIM da ke da alaƙa da Al-Qaeda ta ɗauki nauyin kai harin, sai dai gidan rediyon Nijar ya ruwaito cewa ɓarayin daji ne suka kai harin.
Manyan sojojin Nijar da dama sun halarci jana’izar, daga ciki har da Janar Moussa Salaou Barmou wanda shi ne babban kwamandan hafsoshin Nijar.
Yawan kai hare-hare
Sojojin Nijar da ke kusa da ƙasar Aljeriya na fuskantar hare-hare daga ‘yan bindiga da ke ɗauke da makamai.
Saharar Nijar mai matuƙar girma ta yi ƙaurin suna wurin safarar mutane waɗanda ake ƙoƙarin tsallakawa da su Turai domin neman rayuwa mai kyau.
Ƙasar da ke yankin Sahel na ƙarƙashin mulkin sojoji waɗanda suka ƙwace mulki a Yulin 2023 inda suka sha alwashin samar da tsaro a ƙasar.
Sai dai zuwa yanzu ƙasar na ci gaba da fama da hare-haren ‘yan ta’adda.
Tun bayan juyin mulkin soji a ƙasar, aƙalla mutum 2,400 aka kashe sakamakon rashin tsaro, kamar yadda wata hukuma mai sa ido kan rikice-rikice ta ACLED ta bayyana.
Tare da ƙawayenta Mali da Burkina Faso, ƙasashen sun kafa rudunar haɗin gwiwa mai dakaru 5,000 domin magance rashin tsaro a yankin.