Afirka
1 minti karatu
Dakarun haɗin-gwiwa na AES sun kashe ‘yan ta’adda da kama wasu a Nijar
Dakarun haɗin-gwiwa na ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar sun samu jerin nasarori a samamen da suka kai a Nijar inda suka ƙwace makamai da babura man fetur da dizel da kuɗaɗe daga hannun ‘yan ta’adda.
Dakarun haɗin-gwiwa na AES sun kashe ‘yan ta’adda da kama wasu a Nijar
Dakarun na AES sun ƙwace makamai goma, ciki har da bindigar AK da bindigogin farauta da bindigogin pistol.
3 соат олдин

Dakarun ƙasashen Burkina Faso da Mali da Nijar sun samu nasarar kashe wasu’yan ta’adda da kuma kama wasu a yayin wani samame da suka kai a cikin Nijar.

A yankin Taratakou, dakarun sun gudanar da wani samame wanda hakan ya kai ga kashe wasu ’yan ta’addan ƙungiyar Islamic State in the Greater Sahara wato EIGS.

Dakarun na AES sun ƙwace makamai goma, ciki har da bindigar AK da bindigogin farauta da bindigogin pistol.

Haka kuma dakarun sun ƙwace babura 15 da jarkokin fetur da duro-duro 37 na man dizel.

A yankin Kossa-Tondobo, dakarun na AES sun kama ‘yan ta’adda huɗu inda a nan ma suka ƙwace abubuwa da dama a hannunsu.

Daga cikin abubuwan da suka ƙwace akwai bindigogi uku da babura bakwai da wayoyin Motorola biyu da na’urorin tayar da bam 27 da jarkoki bakwai na fetur.

Dakarun sun kuma kama bandir 40 na tamfal da buhuhunan gero da firji biyu da wayoyin salula biyu da na’urar gano ƙarfe da kuma CFA 22,500.

Wannan ya zama wani babban ci gaba ga dakarun haɗin gwiwar AES a yaƙin da suke yi da ta’addanci da kuma tabbatar da tsaro.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us