Siyasa
3 minti karatu
Dole a tursasa wa Zelenskyy na Ukraine rungumar hanyar zaman lafiya: Russia
Mai magana da yawun Fadar Kremlin Dmitry Peskov ya bayyana cewa, sa'insar da aka ya a Ofishin Oval na Amurka ya nuna wahalar cim ma matsaya.
Dole a tursasa wa Zelenskyy na Ukraine rungumar hanyar zaman lafiya: Russia
Responding to the summit, the Kremlin said the London summit was an attempt to continue the war, not to seek peace, but also noted the divisions between Europe and the US.
3 Machi 2025

Fadar Kremlin ta ce dole ne wani ya tilasta wa Volodymyr Zelenskyy ya amince da batun sulhu, kuma sa’insar da shugaban Ukraine ya yi a bainar jama'a da shugaban Amurka Donald Trump ya nuna irin yadda zai yi wuya a samu hanyar kawo ƙarshen yaƙin.

Kakakin Kremlin Dmitry Peskov ya ce "Abin da ya faru a Fadar White House ranar Juma'a, ya nuna yadda zai yi wahala a cim ma matsaya da Ukraine a nan kusa."

“Gwamnatin Kiev da Zelenskyy ba sa son zaman lafiya. Suna son a ci gaba da yaƙin”.

A ranar Juma'a, Trump da Mataimakin Shugaban kasa JD Vance sun yi sa’insa da Zelenskyy a Ofishin Oval.

Trump ya zargi Zelenskyy da rashin mutunta Amurka, ya ce ya sha kashi a yaƙin kuma yana kasadar haddasa Yakin Duniya na 3.

Peskov ya ce "Yana da matuƙar muhimmanci wani ya tilasta wa Zelenskyy da kansa ya sauya matsayinsa."

"Dole ne wani ya tursasa wa Zelenskyy rungumar zaman lafiya. Idan Turawa za su iya yin hakan, ya kamata a girmama su kuma a yaba musu."

Shugaban kasar Rasha Vladimir Putin ya tura dubban dakaru zuwa Ukraine a shekarar 2022, wanda ya haifar da fada mafi girma tsakanin Moscow da Ƙasashen Yamma tun bayan yaƙin cacar baka.

An shafe shekaru rikici a kan Ukraine yana taruwa kafin yanke shawarar Putin.

A shekara ta 2014 ne Rasha ta mamaye yankin Crimea na kasar Ukraine bayan da aka hambarar da shugaban kasar mai goyon bayan Moscow sakamakon zanga-zangar da aka yi a Kiev.

Daga nan ne 'yan aware da ke samun goyon bayan Rasha suka fara fafatawa da sojojin Ukraine a yankin Donbass na gabashin kasar.

Peskov ya ce Putin ya saba da faruwar "al'amuran da ba a taba ganin irinsu ba" a Ofishin Oval, inda ya ƙara da cewa Zelenskyy kuma ya nuna rashin ƙwarewar a fannin diflomasiyya don ceto alaƙarsa da Trump, amma Ukraine ba za ta bai wa Rasha wani yanki ba a matsayin wani bangare na yarjejeniyar zaman lafiya.

A halin yanzu dai Rasha na da iko na kasa da kashi biyar na Ukraine - ko kuma kimanin murabba'in kilomita 113,000 - yayin da Ukraine ta ƙwace kusan murabba'in kilomita 450 na Rasha a wani kutse a lardin Kursk da ke makwabtaka da ita, bisa ga taswirorin budaddiyar taswirar yakin da kiyasin Rasha.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us