Jam’iyyar Shugaban Chadi Mahamat Idriss Deby ta lashe kujeru 43 daga cikin 46 a zaɓen majalisar dattijai na farko a tarihin ƙasar, kamar yadda sakamakon ƙarshe da aka saki ranar Talata ya nuna.
Zaɓen ‘yan majalisar dattijan na Chadi a ƙarshen Fabrairu shi ne karo na ƙarshe a tsarin komawa mulkin farar-hula, wanda ya fara lokacin da Deby ya hau mulki bayan mutuwar mahaifinsa shekaru huɗu da suka gabata.
Deby ya lashe zaɓen wa’adin shekaru biyar a kan mulki a watan Mayun da ya gabata, a zaɓen da ‘yan hamayya suka ƙauracewa, sannan ƙungiyoyi da ba na gwamnati ba na ƙasa da ƙasa suka ce “ba a yi cikin adalci ba”.
Tuni jami’in na soja wanda a baya bayan nan aka ƙara masa girma zuwa muƙamin Field Marshal, yake ƙoƙarin jaddada ikonsa a ƙasar ta yankin Sahel.
Majalisa mai zaure biyu
Lissafin Majalisar Tsarin Mulkin Chadi na ranar Talata ya tabbatar da cewa an miƙa wa wasu jam’iyyun ƙawance kujeru biyu na ‘yan majalisa waɗanda da fari aka bayyana su a matsayin waɗanda jam’iyyar Patriotic Salvation Movement ta Debby ta lashe.
Har yanzu Deby bai naɗa aƙalla ‘yan majalisar dattijai 23 ba, waɗanda ake buƙatarsu don cike gurbin kujerun majalisar ta dattijai, waɗanda su ne za su wakilci yankuna masu cin gashin kansu.
Gyaran da aka yi ne a 2020 ya kafa majalisa mai zaure biyu, wanda daga baya kundin tsarin mulkin ƙasar da aka yi wa gyara a Disambar 2023 ya tabbatar da shi.