Turkiyya
2 minti karatu
Turkiyya za ta kawar da ta’addanci da samar da makoma mai kyau ga ƙasar — Erdogan
Shugaba Erdogan ya bayyana haka ne a yayin wani taron buɗa-baki da aka shirya wa iyalai da ‘yan uwan ​​shahidai a ranar Asabar.
Turkiyya za ta kawar da ta’addanci da samar da makoma mai kyau ga ƙasar — Erdogan
Erdogan yayin buɗa-baki da 'yan uwan shahidai a Turkiyya
2 مارچ 2025

Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan ya jaddada aniyar Turkiyya ta kawar da ta'addanci a kan iyakokinta da kuma wajenta, yana mai cewa za a ci gaba da gudanar da ayyukan har sai an kawar da 'yan ta'adda na karshe.

Jawabin nasa ya zo ne a yayin wani taron buɗa-baki da aka shirya wa iyalai da ‘yan uwan ​​shahidai a ranar Asabar a daidai lokacin da ƙasar ke kan tsarin kawar da ta’addanci daga Turkiyya wanda hakan ya kai ga ɗaurarran jagoran ƙungiyar PKK Abdullah Ocalan ya yi kira ga ‘yan ta’addan su ajiye makamansu.

Da yake magana kan yaki da ta'addanci da tsaron kasa, Erdogan ya jaddada cewa, duk wani mataki da gwamnatin Turkiyya za ta ɗauka tana ɗaukarsa ne domin kyautata makomar Turkiyya da al'ummarta

Ya ce " Duk matakan da muke ɗauka muna ɗaukarsu ne domin kyautata makomar Turkiyya da al'ummarta,” in ji shi.

Tsayuwar daka kan samar da tsaro

Erdogan ya yi gargadin cewa,  duk da ƙofofin Turkiyya a buɗe suke ga hanyoyin diflomasiya, ba za ta yi kasa a gwiwa ba wajen yin amfani da karfi idan ya cancanta.

“Idan aka yi watsi da hannun da muka mika ko kuma aka cije shi, za mu iya amfani da ƙarfinmu,” kamar yadda ya jaddada

Ya bayyana yadda Turkiyya ke ƙara ƙarfi wajen yaƙi da ta'addanci, inda ya sanya ta a matsayin jagora a duniya wajen yaki da barazanar ta'addanci.

“Ba wai ƙarfi da gwanantaka Turkiyya kaɗai ke da shi a yankinmu wurin yaƙi da ta’addanci ba a cikin gida da waje, amma tana daga cikin mafi ƙarfi a duniya.”

 

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us