Hana karin gashi: Sarauniyar kyau ta Côte d'Ivoire sai mai 'Kyawun asali na Afirka'
Hana karin gashi: Sarauniyar kyau ta Côte d'Ivoire sai mai 'Kyawun asali na Afirka'
Masu shirya bikin zabar sarauniyar kyau ta Côte d'Ivoire sun hana masu takara kara gashi ko saka gashin jabu a wani bangare na ganin an zabi kyawun asali na Afirka, wanda hakan ya janyo muhawara kan 'yancin yin yadda aka ga dama.
21 час назад

Daga Pauline Odhiambo

Rashin gashi mai kyau ba wai matsala ce ta zamanin yau ba - tarihi ma ya nuna cewa rashin kaunar gashin mutum na ingiza jama’ar tsohuwar Masar ga yanke kauna kamar dai yadda suke yi a karni na 21.

Sama da shekaru 5,000 da suka gabata, masu kudi da manyan mutane a Masar na kara gashi ko saka jabun gashi a kawunansu, mahaifar karin gashi. Yi tunani game da Fir’aunoni da sarauniyoyi da masu hannu da shuni.

Har zuwa lokacin da cinikin bayi ya tsananta ma, daga nan ne sai lamarin ya sauya salo. Ana tursasawa matan da ake bautarwa kara gashi ko saka hular gashi don su dace da adon Yammacin Duniya, lamarin da daga baya ya shiga rayuwar bakaken fata a duniya baki daya.

A yanzu, mata ‘yan asalin Afirka ne suka fi yin karin gashi ko saka jabun gashi a kawunansu a duniya baki daya.

GlobeNewswire, wata cibiya da ke fitar da sanarwar manema labarai, ta bayar da rahoton cewa kashi 50 na matan Afirka na yin karin gashi ko saka hular gashi, wadanda wasu da dama kuma suke kara gashi don kare gashinsu na asali daga lalacewa, musamman idan nau’in gashin mai bushewa ko karye wa ne.

Nijeriya da Afirka ta Kudu ne kasashen da suka fi amfani da hular gashi ko kara shi a Afirka. Kamar yadda wasu alkaluma da cibiyar Karin Haske kan Kasuwanci, jarin wannan kasuwanci a nahiyar ya kai dala miliyan 272 a shekarar 2022, wanda aka yi hasashen zai karu zuwa dala miliyan 412.53 nan da shekarar 2030.

Sabon salo

Tun da jimawa karin gashi ya zama wani babban abu a kasuwannin kayan kwalliya, suna samar da duk wani nau’i na gashi da mayar da shi ya dace da duk kamar da ake so.

Wannan lamari ya fi kasancewa tare da gasar kyau, inda masu takara na kabilu daban-daban ke zabar dogo kuma mikakken gashi, suna sake karfafa zabin Turai na dogon gashi maimakon cukurkudadde ko gajere.

Hanin baya bayan nan a wajen gasar sarauniyar kyau ta Côte d'Ivoire ya yamutsa hazo game da wannan abu da suke saka wa a kai.

A ranar 28 ga Janairu, wadanda suka shirya bikin sun yanke hukuncin girgiza abubuwa ta hanyar bayar da umarnin tirsasawa ‘yan takarar kyawun fitowa da gashinsu na asali, ko dogo, ko gajere, ko mai kitso, wanda aka tattare ko aka aske.

A yayin da suke nuna muhimmanci da bikin bayyana tsantsar kyawun Afirka na asali mai inganci, shugaban kwamitin shirya gasar sarauniyar kyau tna Côte d'Ivoire, Victor Yapobi, ya bayar da misali ga wadanda suka lashe gasar a baya da cewa suna da gajeren gashi kuma nasu na asali.

“Dole ne dukkan ‘yan takara da ke son shiga gasar sarauniyar kyau ta Miss Côte d'Ivoire su zo da gashinsu na asali,” in ji Yapobi a babban birnin Abidjan a yayin da ake gab da fara gasar.

“Wannan sauyi ya faro ne daga lura da cewa muna yawan kalubalantar amfani da gashin jabu ko kara gashi, wanda tsarinsa da yin sa ba ya cikin al’adun Côte d'Ivoire.”

Mariene Kouassi, sarauniyar kyau ta Côte d'Ivoire a 2022 ce ta yi tasiri wajen tabbatar da wannan sabon sharadi. Ta halarci gasar a wannan shekarar da gajeren gashi.

Nuna soyayya ga kai

Matakin na da manufar karfafa wa gwiwa mata su dinga dogara kan kyawunsu na asali mai makon wasu kayayyaki na jabu.

Yapobi ya bayyana cewa babbar manufar sabuwar dokar sarauniyar kyau ita ce habaka nuna soyayya ga kai da karfin zuciya a tsakanin ‘yan takarar, yayin da ake kuma karfafa wa matan gwiwa da su rungumi amfani da gashinsu na asali.

Duk da cewa wasu masu takarar zama sarauniyar kyau a Côte d'Ivoire na cewa matakin ya dace, amma masanin zamantakewar dan adam Gnelbin Nicaise Hlil na da ra’ayin cewa sau da yawa alamomin kyau a hankali suke bayyana.

“Gaskiya ne wannan mataki ne na habaka gashi na asali da ake da shi tsawon lokaci. A lokaci guda, idan muka lura da al’umma, za mu ga cewa wasu dabi’unsu ba su bace ba. Batun kara hasken fata bai kau ba har yanzu, kamar yadda karin gashi ko saka hular gashi jabu su ma ba su kau ba,” in ji Hlil

Martani daban-daban

Mutane da dama sun bayyana mataki na hana karin gashi a yayin gasar sarauniyar kyau ta Côte d'Ivoire a matsayin lamari na ‘tarihi’, duk da cewa wasu na cewa wannan keta kakki da ‘yancin mutum ne.

“Côte d'Ivoire ta saka dokoki kuma na yi imanin sauran kasashe ma za bi sawu nan da wani dan lokaci,” Linda Karanja ‘yar Kenya da ke bibiyar gasar sarauniyoyin kyau na duniya, ta fada wa TRT Afrika.

Marguerite Koutouan, wata mai gyaran gashi a Abidjan, ta yi nuni da cewa daina amfani da hular gashi ko karin gashi na kawar da hatsarin cutar da kokon kan mutum.

“Wasu gashin da hular gashi na janyo cutar da ake kira alopecia da illata kokon kai da ba a iya gyara shi saboda saka gashin ba ta hanyar da ta dace ba da gam mai karfi da ake amfani da shi. Yanzu, sarauniyoyin kyau namu za su iya yawo da gashinsu na asali da kuma magance zubewar gashi,” in ji ta.

Dan kasuwar Nijeriya, Karim Aboubakar ya bayyana cewa gara a bar ‘yan takarar da kansu su zabi me za su saka ko yaya gashinsu zai zama.

Ya fada wa TRT Afrika cewa “Fararen fata, da ‘yan Asiya da Latin da ke shiga gasar kyau ma na saka hulunan gashi don kara tsayin gashinsu, janye wannan ‘yanci wata hanya ce ta zaluntar mata bakar fata.”

Wasu sauye-sauyen da aka yi wa dokokin gasar sarauniyar kyau a Côte d'Ivoire sun hada da mafi karancin tsayi da aka kayyade kan mita 1.68 zuwa 1.67. An kuma sake duba shekaru daga 25 zuwa 28.

Har nan da 1 ga Mayu za a ci gaba da tantance wadanda za su shiga gasar sarauniyar kyau ta Côte d'Ivoire ta 2025 inda za a zabi wanda ya yi nasara a ranar 26 ga Yuni.

TUSHEN:TRT Afrika
Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us