Mawakin zamani na Afrobeats na Nijeriya Asake ya sake samun nadin shiga takarar neman lashe kambin iya waka na 'Brits Awars 2025' a bangaren Mawakan kasa da Kasa a karo na biyu, wanda hakan yake da muhimmanci ga ci gaban sana'arsa.
Asake na fuskantar gogayya mai zafi fannin Mawakin Kasa da Kasa, inda yake tafiya kafada da kafada da wasu manyan mawaka a duniya, irin su Beyonce da Tayor Swift, wadanda dukkan su suna da dogon tarihi na nasarar lashe Kambin 'Brits Awards'.
A shekarar da ta gabata, Asake ya shiga takarar neman lashe matsayin Mafi Iya Waka na Kasa da Kasa tare da Burna Boy da Rema, amma dukka ukun ba su yi nasarar lashe kambin ba.
Wasu da ke neman lashe kambin su ne Billie Eilish, da aka san ta da murya ta musamman da mabiya da yawa a duniya, da tauraro mai haskakawa Benson Boone.
Asake bai yi wani bayani a bainar jama'a ba game da wannan nadi, amma labarin ya yadu a shafukan sada zumunta tun bayan fitar da sanarwar a ranar Alhamis.
Wakokin Asake, da suke gamayyar salon wakokin Afrobeats da Fuji, na jan hankalin masu sauraro a duniya.