Afirka
2 minti karatu
Rundunar Sojin Sudan ta ƙwace wata muhimmiyar gada a Khartoum
Sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce dakarun sojin sun sake ƙwace iko da gabashin gadar Manshia da ke gabashin birnin Khartoum.
Rundunar Sojin Sudan ta ƙwace wata muhimmiyar gada a Khartoum
Tun watan Afrilun 2023 aka fara yakin Sudan
5. März 2025

Sojojin Sudan sun ƙwace gefen gabashin wata gada mai muhimmanci a Khartoum babban birnin kasar a ranar Talata daga hannun dakarun Rapid Support Forces (RSF).

Sanarwar da rundunar sojin ta fitar ta ce dakarun sojin sun sake ƙwace iko da gabashin gadar Manshia da ke gabashin birnin Khartoum.

Sojojin sun fitar da wani bidiyo da ke nuna wani kwamandan soji yana duba dakarunsa a bakin gadar.

Gadar Manshia ita ce gada ta ƙarshe da RSF ta riƙe a kan kogin Blue Nile.

An ƙwace ikon gadoji tara

Sojojin sun sake ƙwace iko da gadoji tara da suka hada muhimman birane uku a birnin Khartoum, in ban da gadar Jebel Aulia da ke gabar Kogin White Nile a kudancin Khartoum.

Kawo yanzu dai babu wani karin haske daga kungiyar ta RSF kan sanarwar sojojin.

A ranar Litinin sojojin sun kutsa cikin yankin Gabashin Nile da ke birnin Khartoum tare da kame wasu wuraren gwamnati a can.

Sojojin Sudan sun samu gagarumar nasara ta soji kan bangaren 'yan tawaye a yankuna da dama a cikin 'yan watannin nan.

Adadin wadanda suka mutu a yakin

A jihar Khartoum mai ƙunshe da garuruwa uku, a halin yanzu sojoji suna iko da garin Bahri a arewa, mafi yawan Omdurman a yamma, da kuma kashi 75% na birnin Khartoum, inda Fadar Shugaban Ƙasa da filin jiragen sama na kasa da kasa suke.

Duk da haka, har yanzu RSF na ci gaba da kasancewa a yankunan gabashi da kudancin Khartoum.

Kasar Sudan dai ta fada cikin yaƙi tsakanin sojojin Sudan da kungiyar RSF tun a tsakiyar watan Afrilun shekarar 2023, inda aka kashe sama da mutum 20,000 tare da raba miliyan 14 da muhallansu, a cewar MDD da hukumomin kasar.

Bincike daga jami'o'in Amurka, ya kiyasta adadin wadanda suka mutu ya kai kusan 130,000.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us