An bayyana yawan kuɗin kyauta da za a bayar a gasar kulob-kulob ta duniya ta 2025, wadda za a yi tsakanin ƙungiyoyi 32. Kuɗin da ya ka dala miliyan ɗaya, kuma shi ne adadi mafi girma da za a bayar a tarihin gasar.
Ba a fayyace ta inda FIFA za ta samo kuɗaɗen ba, sai dai hukumar ta samu kudin ɗaukar nauyi na lasisin watsa shirye-shiryen gasar tun a watannin baya.
A Disamban bara, kamfanin yaɗa shirye-shirye ta intanet da ke London, DAZN ya samu haƙƙin mallakar watsa gasar, kan kwantiragin da ya kai kusan dala biliyan ɗaya.
Wasanni 24 cikin 63 da za a buga a Amurka, tashar TNT Sports za ta yaɗa su, inda ƙungiyoyi kamar Inter Miami da Paris Saint-Germain saboda masoyansu Amurkawa.
Haka nan kuma, FIFA ta samu kwantiragin ɗaukar nauyi daga manyan kamfanoni kamar Coca-Cola, Bank of America, da kamfanin kayan lantarki na China, Hisense, da kuma kamfanin giya na Belgium, AB InBev.
Rabon kuɗi
Kuɗin da za a bayar a gasar ya zarga yawan wanda aka taɓa bayarwa a baya a gasannin kulob-kulob na FIFA na maza ko na mata, da fifiko mai girma.
Za a raba kuɗin ne ta hanyar biyan kuɗin halarta ga ƙungiyoyi, da kuma na kai wa wani mataki a gasar.
Shafin Goal ya ambato jaridar The Independent tana cewa za a ba da dala miliyan 575 ga mahalarta, sai kuma dala miliyan 465 gwargwadon ƙoƙarin ƙungiya.
Sai dai kuma, ba za a raba kuɗin halartar daidai wa daidai ga ƙungiyoyin ba. Za a raba ne ta hanyar hukumomin ƙwallo na yankuna, saboda daidaitawa za ta haifar da mabambancin tasiri tsakanin sassan duniya.
Alal misali, Manchester City da Chelsea, za su iya samun dala miliyan 60-90 daga gasar. Sannan FIFA za ta ba da ladan ganin-ido da ya kai aƙalla dala miliyan 150 ga ƙungiyoyin da ba su halarta ba.
Gasar kulob-kulob ɗin ta 2025 za ta gudana ne a wurare 12 a birane 11 na Amurka, inda za a buga wasan ƙarshe a filin wasa na MetLife Stadium, a birnin New Jersey, wanda a nan ne za a buga wasan ƙarshe na Kofin Duniya na 2026.