Turkiyya
2 minti karatu
Bututun Igdir-Nakchivan zai haifar wa shirin Turkiyya da Azerbaijan kyakkyawan sakamako — Erdogan
‘A yau, muna kawo wa ƙasashenmu wani aiki wanda zai tabbatar da samar da makamashi a shirin Nakhchivan na tsawon lokaci,’ a cewar Recep Tayyip Erdogan.
Bututun Igdir-Nakchivan zai haifar wa shirin Turkiyya da Azerbaijan kyakkyawan sakamako — Erdogan
Erdoan ya ce Ankara da Baku sun kudiri hada kai domin aiwatar da kowane irin aiki don samar da zaman lafiya da ci-gaba da daidaitar al’amura a yankin.
7 hours ago

Aikin Bututun Gas na FIgdir-Nakchivanzai kawo gagarumin ci-gaba a shirin fannin makamashi tsakanin Turkiyya da Azerbijan, a cewar Shugaban Turkiyya Recep Tayyip Erdogan.

“A yau, muna tabbatar da wani aiki domin ƙasashenmu wanda zai tabbatar da samar da makamashi ga shirin Nakhchivan na tsawon lokaci,” a cewar Erdogan a ranar Laraba a jawabin da ya yi ta bidiyo ga taron ƙaddamar da bututun tare da Shugaban Azerbijan Ilham Aliyev.

Erdogan ya ce Ankara da Baku sun ƙuduri haɗa kai domin aiwatar da kowane irin aiki domin samar da zaman lafiya da ci-gaba da daidaitar al’amura a yankin.

Haɗa kan Turkawa

Erdogan ya ce ƙasashen Turkiyya da Azerbaijan suna ɓangaren “zaman lafiya da kwanciyar hankali da ci-gaba,” inda ya ƙara da cewa: “Zaman lafiya kawai muke so a yankinmu. Muna son haɗin kai don bunƙasa tare.”

A nasa ɓangaren, Aliyev ya ce aikin butun mai da na gas ba kawai ya haɗa kan Turkiyya da Azerbaijan ba ne, ya ma sauya taswirar makamashi ta nahiyar Turai da Asia.

Ya ce haɗin kai tsakanin Ankara da Baki wata gagarumar gudunmawa ce ga duniyar Turkawa, yana mai yaba wa Erdogan saboda rawar da ya taka wajen haɗa kan al’ummar da ke magana da harshen Turkanci.

Duba a TRT Global. Raba ra'ayinka!
Contact us