Isra’ila ta ce ta amince da tsagaita wuta na dan wani lokaci a Falasdinu a watan Ramadana da lokacin bukukuwan Yahudawa na Passover, bayan shawarar da Jakadan Amurka a Gabas ta Tsakiya Steve Witkoff ya bayar, sa’o’i gabanin wa’adin kashin farko na tsagaita wutar ya kare.
Ofishin Firaministan Isra’ila Benjamin Netanyahu ya fada a cikin wata sanarwa cewa za a saki rabin wadanda aka yi garkuwa da su a Gaza a mace ko a raye, sannan za a saki ragowar wadanda ake tsare da su da zarar an cim ma yarjejeniyar tsagaita wuta ta dindindin
Ta ce Witkoff ya ba da shawarar tsawaita wa’adin tsagaita wutar bayan yanke hukuncin cewa ana bukatar karin lokaci don tattaunawa kan tsagaita wuta ta dindindin.
Sanarwar ta ce shirin ya bai wa Isra’ila ‘yancin ci-gaba da yaki bayan kwanaki 42 idan babu ci-gaba a tattaunawar da ake yi, sannan ta yi da’awar cewa Isra’ila ta amince da shawarar sakin fursunoni amma Hamas ba ta amince ba har yanzu.
Ta jaddada cewa idan Hamas ta sauya matsayarta ta kuma karbi shawarar ta Witkoff, nan take Isra’ila za ta fara tattaunawa kan matakan kashi na biyu na tattaunawar.
Har yanzu masu shiga tsakani na Hamas da Masar da Qatar da ma Witkoff ba su ce komai ba kan sanarwar ta Isra’ila.
Tun da farko mai magana da yawun kungiyar gwagwarmayar ta Falasdinawa Hazem Qassem ya fitar da wata sanarwa inda a ciki ya jaddada “kudirin aiwatar da duka matakan tsagaita wutar da aka tsara.”
Tun daga watan Janairu yarjejeniyar tsagaita wuta da kuma musayar fursunoni ke aiki, abin da ya sa Isra’ila ta dakatar da yakin kare dangin da take yi a Gaza, wanda ya kashe fiye da mutane 38,360, mafi yawancinsu mata da yara, sannan ya bar yankin zirin Gaza a cikin mummanan yanayi.